Lantarki ya ragu da kashi 1.64 a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bangaren wutar lantarkin Nijeriya ya ragu a ƙarshen shekarar 2024, inda samar da wutar lantarki ya ragu da kashi 1.64.

Bayanai daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun ce wannan ya nuna an samu koma baya daga ƙaruwar kashi 5.55 da aka samu a tsakiyar shekarar 2024.

Matsakaicin kiyasin samar da wutar lantarki ya ƙaru da 2.34 zuwa megawatts 4,206.50 a kowace awa daga 4,110.47 a tsakiyar shekarar 2024.

Hakazalika, amfani da wutar lantarki ya samu ƙaruwa kaɗan da kashi 2.63, inda ya kai 4,105.66 MW/h daga 4,000.24 MW/h.

Hakan ya kasance ne yayin da tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka a ƙarshen shekarar 2024, tare da kashi 21 cikin 22 da ke samun ci gaba mai kyau.

Manufofin gwamnati na kasafin kuɗi da nufin daidaita hauhawar farashin kayayyaki da haɓaka zuba jari, suma sun ba da gudunmawa ga ci gaba mai kyau.

A cewar babban bankin CBN, an samu wannan ci gaba ne saboda inganta samar da iskar gas ga tashoshin wutar lantarki da kuma ci gaba da aiwatar da aikin samar da wutar lantarki na Siemens, wanda ya yi tasiri sosai wajen samar da wutar lantarki, watsawa, da hanyoyin rarraba wutar lantarki.

Musamman ma, ɓangaren mai da iskar gas ya amfana daga ingantaccen farashin danyen mai da kuma inganta samar da kayayyaki a cikin gida, wanda ya ba da habaka ga ci gaban tattalin arzikin kasa baki ɗaya.

By ukarofi