Kuɗin shigar DStv ya ragu sakamakon asarar kwastamomi miliyan huɗu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Multichoice, babban kamfanin talbijin na Afirka, ya buƙaci masu hannun jarinsa da su shiryawa afkuwar matsaloli masu yawa a nan gaba, saboda yana aiki a cikin mawuyancin yanayi.

MultiChoice, wanda ke da DStv, ya ga kwastamominsa sun ragu daga sama da miliyan 23 zuwa miliyan 19.3 a cikin ƙasa da shekaru biyu.

Majiyoyin cikin gida sun ce, babban kaso na asarar kwastamomi ya faru a wajen gidansu na Afirka ta Kudu kuma sama da kashi 84 na abokan cinikin DSTV ne.

A cikin wata sanarwa da ma’aikacin gidan talabijin ɗin ya fitar a baya ya ce “rashin da aka samu a sauran ƙasashen Afirka ya samo asali ne saboda tsananin matsin lambar da masu amfani da kayayyaki ke fuskanta a Nijeriya, inda hauhawar farashin kayayyaki ya kasance sama da kashi 30 cikin 100 a mafi yawan watanni 12 da suka wuce, kuma a baya-bayan nan, saboda taɓarɓarewar wutar lantarki a Zambia.”

A cikin sabuntawar ayyukansa, kamfanin ya ce yana shirya sakamakon kuɗin sa na shekarar da za ta ƙare 31 ga Maris 2025.

Sanarwar ga masu hannun jarin ta ce aalubalen yanayin masu amfani ya haifar da raguwar masu biyan kuɗi da ƙarancin haɓakar kuɗaɗen shiga.

By ukarofi