Larurar Dannau a likitance (Sleep Paralysis)

Tare da Chiroma Aminu Asid

Dannau wani yanayi ne da mutane kan samu kansu a halin bacci, ya kan iya faruwa sau ɗaya ga wasu a rayuwa, yayin da wasu kuma kan riƙa fuskantar yanayin akai-akai.

Yanayi ne mai kama da mutuwa, duk da ya kan kasance mutum na a cikin hayyacinsa a farke sai dai sam ya kan rasa ikon motsawa ko magana. Wani lokacin ma ya kan zamo idon mutum a buɗe a zahiri duk da cikin bacci yake; abunda wasu kan kira da baccin zomo.

To, sai dai hakan duk bai sa mutanen dake kusa ko yake jin muryarsu fahimtar cewa, yana cikin mawuyacin hali ko yana buƙatar ɗauki an maƙure shi. Shi ya sa ga duk mai son fahimtar me ake nufi da ‘firgici’ to, Dannau shine cikakken misalin firgici ko na ce ihunka banza, domin ko ihun ka yi ba a ji, ba a san ma ka na yi ba. 

Alamomin Dannau:

Mutane kan fuskanci mabambantan alamu; sai dai duk yana daga alamun Dannau ya zamto:

Mutum ya ji kamar an nan-naɗe shi cikin wani bargo mai nauyi, ko kamar an ɗaure hannuwa da ƙafafunsa a miƙe kamar gawa, wasu kuma su ji kamar an shaƙe su sun kasa numfashi, wasu kamar wani abu ya kakare musu a maƙogoro sun kasa shaƙar iska, wasu kan ji sun kasa magana, wasu kuma su a karan-kansu su ji suna maganar, amma kuma babu wanda yake jin su, sukan kasa motsa komai nasu, wasu kan riƙa jin tamkar mutuwa ce ta kusanto su

Meke haddasa Dannau?

ɗaya daga manyan ababen da ke haddasa hakan shine;

ƙarancin bacci, wato mutane masu fama da larurar rashin bacci ko kuma waɗanda suke ƙin kwanciya su samarwa da jikinsu isashshen bacci. Haka nan samun canjin lokutan bacci kai tsaye wataƙila, saboda yanayin aiki ko tafiya zuwa wata ƙasa da lokaci ya bambanta sosai. Haka nan shan wasu magunguna dake aiki a ƙwaƙwalwa, kamar a mutane masu ciwon farfaɗiya, larurar halayya (personality disorders) ko kasancewa cikin tsananin halin matsi ko gajiya, wato ‘stress’ a koda yaushe, ko larurar hawan jini, ko larurar damuwa, wato ‘depression’, duk suna iya haddasa Dannau. Sai kuma halayyar kwanciya ta rigingine, wato ta gadon baya fuska na kallon sama.

Sai mutane masu shan ƙwayoyi ko magunguna masu sanya maye. Sai dai galibi mutane masu fuskantar ƙarancin bacci sun fi fuskantar wannan matsala sama da sau 10 fiye da saura. Daga nan sai masu kwanciya ta gadon baya fuska a sama.

Yaushe Dannau ya fi faruwa?

Ya fi zuwa da safe ko da gabannin asuba, ko masu irin koma wa baccin nan bayan sun yi sallah irin ƙarfe 6:00 na safe ɗin nan. Hakan na faruwa ne walau a farkon bacci, wato wato sannan mutum ya kwanta ba tare da jimawa ba, inda ya kan ga abun tamkar na faruwa ne a tunani ba zahiri ba, saboda sanda bacci ya fara dɗaukar ka ba ka sani sai dai ka ji ka shiga baccin kai tsaye, amma idan ya zamto ka fara bacci, amma ka na jin tafiyarka zuwa cikin baccin ‘counsiciously’, to, a lokacin za ka ji ka kasa magana ko motsi. Yadda Dannau ke zuwa kenan.

Sai kuma ƙarshen bacci, wato gab da farkowa, domin sanda bacci ya zo ƙarshe duk da idanuwanka suna rufe ƙwayar idonka ke fara farkowa, wanda hakan zai sa idanuwan su riƙa kaɗawa, sosai yayin da duk sauran jikinka yake a sake, wato ‘relaɗed’. A daidai wannan lokaci ne mafarki kowanne iri kan zo. To, Idan ya zamto idanuwan sun fara ‘process’ ɗin zai ci gaba da gangaro wa tsokokin wuyanka, kafaɗunka zuwa hannayenka, gadon baya, sannan ƙafafunka, sai ka ji ka farko har da yin miƙa.

To, amma idan bayan farkowar idanun jikinka ya cigaba da zamo wa ‘relaɗed’, wato ya yi jinkirin farkawa, saboda ‘position’ ɗin da ka ke ko kuwa bacci bai isa ba, wata larura ce ta farko da kai, hakan ke haddasa Dannau. Sai ka ji idonka biyu, amma sauran jikinka ya ƙi farkowa.

Yadda ake magance matsalar Dannau:

Babu wani gwaji da likitoci ke yi, domin gano Dannau. Sai dai ga wanda abun ya tsananta akai-akai ta kai ga har numfashinsa na ɗaukewa, a kan binkici mutum ko yana ɗauke da wata damuwa, don a ba shi maganin da zai kawar da ita ko shawarwari, ko magance hawan jinin ya zamto ‘under control’ ko yaushe:-

-Kyakkyawan shirin kwanciya, wato ya zamto kaya ba masu nauyi ba a jika, sannan a yi alwala, inda hali ga maza ko mata ko da ana cikin haila tare da addu’o’i yayin kwanciya. Hakan na sanya jiki samun nutsuwa da aminci ko da cikin halin tsoro ake. -ƙaurace wa kwanciya ta rigingine. Galibi wannan shine dalili ga mutanen da ke kwance ta gadon baya fuska na kallon sama. Don haka ku kwanta a kowanne ‘position’, amma banda rigingine, za ku ji kun daina da ikon Allah.

-Gyarawa tare da ɗorewa bisa tsarin bacci mai kyau da zai sa ka riƙa samun baccin awa 6 zuwa 8 a rana ko a dare. Ko me ka ke yi, idan lokaci ya yi rufe wayar nan ko kuwa ka saita ta ‘automatic’ ta riƙa rufe kanta.

-Tabbatar da ingantacciyar tsaftar gurin kwanciya. Aƙalla duk sati a riƙa canja zanin gado da rigar filo. A riƙa sharewa tare da kakkaɓe gurin kwanciya kullum.

-Baccin rana, musamman tsakanin ƙarfe 1:30 zuwa 2:30 na rana, idan an sami lokaci, kada baccin rana ya riƙa wuce awa ɗaya da rabi tare da ƙaurace wa kwanciya bayan ƙarfe 3:00 na rana har zuwa Magariba. Baccin yamma ba abu ne mai kyau ba sam, sai dai larura.

-Banda cin abinci mai nauyi ko motsa jiki ƙasa da awa 2 kafin lokacin kwanciya bacci.

-Banda amfani da ‘electronic items’; su waya da sauransu awa aɗay kafin kwanciya bacci. Wasu ma’auratan ma kan sa wa kai dokar hana shiga ɗakin bacci da waya sam, don a sami lokacin juna.

-Cikakken tsaftar baki. A riƙa goge baki (brush) da kyau, domin wasu bakinsu kan samar da miyau ɗin bacci, wanda idan suka kwanta a rigingine miyau ɗin ne ke toshe kafar numfashinsu, wanda wannan abun tsoro ne; shine mutuwa ka iya zuwa idan abun bai saki mutum a kan kari ba.

Muddin aka kiyaye wannan, za a riƙa kwana lafiya.

Menene abin yi yayin da Dannau ke afkuwa?

Galibi yana zuwa cikin hayyaci ga mutane, suna yin tunani tare da komai, kurum motsi ko magana ke gagarar mutum. Don haka abin da ya kamata ka yi yayin da ka ji wannan ɗaurin kazar kukun:

-A riƙa yin salati, ka sanar da Ubangiji shine matakin farko.

-Ka yi ƙoƙarin amfani da tsokokin idanunka, wato ka jarraba runtse idonka ‘tight’ ka rufe su, ka riƙa buɗewa a hankali. Ka yi ta maimaita haka.

-Idan ka na iya yin numfashi, to ka shaƙi iska ‘deeply’, wato ka yi irin shaƙar iskar nan ba tare da ka tsaya fitar da ita ba har sai cikinka ya ɗago. Idan ka yi haka ƙila sai dai ka ji kamar an yaye ma ka labule, ka farko.

-Ka na iya jarraba sanya wa ranka cewa, ga shi nan ka na ƙoƙarin motsa yatsun hannunka da na ƙafa. Ka jarraba amfani da yatsun farko kafin sauran sassan jiki hannu, ƙafafu da sauransu.

-Idan ya kasance a cikin yanayin ka na jin motsi ko muryar mutane ko kuwa wani ne ma da ka sani ka ji yana danne ka a baccin, to, ka canza wannan ‘feelings’ ɗin zuwa cewa, wannan ɗin fa da ka ke jin muryarsa ƙoƙari ya ke ya tashe ka.

-A duk irin yanayin da ka sami kanka na Dannau ka yi ƙoƙarin tunano wani abun muhimmi, ka canza yanayin da shi har zuwa sanda za ka farko.

-Sannan ka zamo mai jaddada kalmar shahada ko Ayatul Kursiyyu.

Danna zuwa yanzu a kimiyyance:

Babu wani sananne, wanda ya mutu a dalilin lalurar Dannau ko ya haɗu da wata illa. Yanayi ne kurum da ya ke buƙatar haƙuri da kwantar da hankali. Mafi tsayin lokacin da za ka yi a haka bai wuce mintuna uku. Sai dai tabbas akwai firgici, domin ka na iya farkowa ka ji ka na zufa ko zuciyarka na bugawa farfar! Sannan babu wani alamu da ke nuna aljani ne gaskiya, saboda mutanen da kan camfa haka ko zargi ga aljanu ko mayu da sauransu, kamar yadda ku ka ji na ce ‘DISRUPTION’ ne na ‘REM SLEEP’, saboda haka ai wasu dukkan adduo’i suna yi kafin kwanciya, amma za ka ga duk da haka suna fuskantar lamarin.

Allah ya tsare mu.

Aminu Asid ma’aikacin lafiya ne a Jihar Kano