
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, ta tabbatar mutuwar mutane biyu yayin da wasu 15 suka samu raunuka a lokacin da wani gini mai hawa uku ya rufta masu a layin 3 Oremeta dake yankin Ojodu a Jihar Legas.
Kodinetan NEMA na shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar, inda Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar, LASEMA, ta samu kiraye-kiyaren kai ɗauki.
Ya ce, kawo yanzu jami’ansu suna ƙoƙarin ceto rayuka da dukiyoyin da abin ya shafa.
Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunukan asibiti, yayin da ake ƙoƙarin gano musabbabin faruwar al’amarin.
