NELFUND: Ɗalibai sun koka yayin binciken badaƙala a jami’o’i

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Hana Rashawa da Makamantanta, ICPC, ta fara binciken wasu jami’o’i da bankuna ganin yadda ɗalibai suka gaza samun kuɗaɗe daga Shirin Asusun bada Lamunin Kuɗin Karatu ga Ɗalibai, wato NELFUND da Gwmantin Tarayya ta ƙaddamar.

Hakan ya biyo bayan ƙudirin Majalisar Wakilai ne na gudanar da bincike game da zargin wasu jami’o’i da bankuna da riƙe kuɗaɗen da aka ware don tallafa wa ɗaliban.

Hukumar Wayar da kan Al’umma, NOA ta bankaɗo wani aikin rashin gaskiya a yayin aiwatar da shirin, inda da dama daga ciki makarantun sun riƙe kuɗaɗen.

A shekarar 2024 ne Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ta kafa shirin a ƙoƙarinta na cika alƙawarin da ta ɗauka yayin neman zaɓe don inganta karatun gaba da sakandare ga ɗalibai, lamarin da ya sa aka ware biliyan N35 a karon fari.

Shirin NELFUND ya na tura kuɗaɗen karatu ne kai-tsaye ga makarantu, yayin da kuma ya ke sanya alawus na N20,000 a kowane wata ga asusun ɗalibai.

NOA ta hannun Mataimakin Daraktan yaɗa labaranta, Paul Odeniyi, ta tabbatar da cewa, wasu makarantu da haɗin-gwiwar bankuna, suna hana ruwa gudu a shirin wajen ƙin sake kuɗaɗen kai wa ga ɗaliban, waɗanda saboda su aka ware su.

Tuni ICPC ta ofishin Kakakinta, Demola Bakare ta ce, ta fara gudanar da bincike a kai da ƙoƙarin ɗaukar matakan da suka dace akan waɗanda aka same su da hannu aciki.

By Babaji