Daga AISHA ASAS
A ƙoƙarin kawo gagarumin cigaba a masana’antar finafinai ta Nijeriya, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin Hukumar Kula da Gidajen Tarihi, wato NCMM, ta ba wa kamfanin Lenscope Media aikin gina gidan shirya finafinai na Jos, wato Film ɓillage, tare da haɓaka wasu wuraren tarihi da ke Zariya, Kano da kuma Katsina.
Aikin wanda aka sa hannu kan sa a ranar 7 ga watan Fabrairi, na wannan shekara zai mayar da hankali ne kan mayar da wasu wuraren wasan kwaikwayo wurin horas da ‘yan wasa da sauransu. sannan za a yi ginin ne a wani ɓangare na gidan tarihin gine-ginen gargajiya, wato MONTNA.
A ɓangaren Kano kuwa, Lenscope zai tada gidajen tarihi irin su, Bangon Birnin Kano, yayin da za a tayar da Masallacin Juma’a a Zariya. Katsina kuwa Fadar Sarkın Katsina.
A ranar Alhamis, 6 ga watan Fabrairu, 2025, aka sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma kamfanoni masu zaman kansu, wato PPP, kamar dai yadda Manhaja ta ruwaito a makon da ya gabata.
Da yake wakilcin Lenscope Media a wurin bikin, Shugaba Makama Sani Muazu ya jaddada aniyar ƙungiyar na yin amfani da ƙwararrun masana’antu don sake dawo da wuraren tarihi don amfana da fasaha da ƙirƙira. Barista Babatunde Adebiyi ne ya sanya hannu kan kwantiragin, yayin da Darakta-Janar na NCMM, Mista Olugbile Holloway, ya bayyana kwarin gwiwa kan yadda Kamfanin Lenscope Media zai gudanar da aikin.
A wani ɓangare na sake fasalin, Kamfanin Lenscope Media zai sake gina katafaren wuraren tarihi da suka haɗa da katangar birnin Kano, da Masallacin Juma’a na Zariya, da kuma Fadar Sarkin Katsina, wadda ake yawan amfani da ita a finafinai na Najeriya da sauran ƙasashen duniya. Kuma waɗannan gine-ginen tarihi za a shigar da su ƙarƙashin Gidan Shirya finafinai na Jos, wanda zai ƙara inganta sahihancin shirye-shiryen finafinai tare da kiyaye al’adun gargajiya.
Bayan shirya finafinai, sabon Film ɓillage na Jos zai ƙunshi wani gidan cin abinci na Arewa, wanda zai samar da kayan abinci masu tarin yawa na Arewacin Najeriya, da kuma wuraren dawaki na sana’ar finafinai na musamman, wanda zai ƙara jawo hankalin masu shirya finafinai da masu yawon buɗe ido, tare da zuba jarin farko na miliyan 250, a ƙoƙarin ganin shirin na bunƙasa tattalin arzikin cikin gida, samar da guraben aikin yi ga dubannan matasa masu hazaƙa, da kuma ƙarfafa matsayin Jihar Filato a matsayin wata muhimmiyar makoma ga masu shirya finafinai a faɗin Afirka.
Da zarar an fara aiki, ana sa ran Gidan Shirya Finafinai na Jos zai inganta harkar shirya fim, da inganta al’adun gargajiya, da zaburar da ci gaban yawon buɗe ido a Najeriya.