Li Keqiang: Sin za ta rungumi salon cigaba bisa daidaito a fannin cinikayyar waje

Daga CMG HAUSA

Firaministan ƙasar Sin Li Keqiang ya ce, gwamnatin Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufofin bunƙasa cinikayyar waje, a matsayin ɗaya daga ginshikan daidaitawa, da inganta rayuwar alummar ƙasar.

Hakan dai sakamako ne na taron majalissar gudanarwar ƙasar Sin, wanda firaminista Li Keqiang ya jagoranta a jiya Laraba. Kaza lika taron ya amince da buƙatar aiwatar da manufar tallafawa hada-hadar fitar da hajoji zuwa ƙetare, domin bunƙasa cinikayyar waje ta Sin.

Har ila yau, an amince da aiwatar da matakan daƙile tasirin annobar COVID-19, da bunkasa farfadowa da ci gaban sayayyar hajojin waje.

Taron ya ce, domin sauƙaƙa wahalhalun da kamfanonin ƙetare ke fuskanta yayin cinikayya, da burin bunƙasa daidaito a fannonin shige da ficen hajoji, za a ƙara inganta matakan samar da rangwame a fannin haraji, mai dacewa da dokokin ƙasa da ƙasa, tare da kara inganta yanayin muhallin gudanar da hada-hadar kasuwanci da sassan ƙetare daga ɓangarori daban daban.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan