Li Keqiang ya jaddada muhimmancin sanya sabon kuzari don samar da cigaba

Daga CMG HAUSA

Daga ranar 16 zuwa 17 ga watan nan, firaministan ƙasar Sin Li Keqiang, ya ziyarci birnin Shenzhen na lardin Guangdong dake kudancin ƙasar Sin, inda ya jaddada cewa, ya dace a bi ra’ayin jagorancin shugaba Xi Jinping, irin na gurguzu mai salon musamman na ƙasar Sin a sabon zamanin da muke ciki.

Da tabbatar da sabon ra’ayin samar da ci gaba, da daidaita ayyukan kandagarkin annobar COVID-19, da raya tattalin arzikin ƙasa, da ci gaba da aza tubali mai inganci na farfado da tattalin arzikin ƙasar, a wani ƙoƙari na tabbatar da samar da guraben ayyukan yi ga al’umma, da kyautata rayuwarsu ta yau da kullum, don raya tattalin arziki yadda ya kamata.

Li ya ce, buɗe ƙofa ga ƙasashen waje, babbar manufa ce ta ƙasar Sin, kana, komai sauyawar halin da ake ciki a ƙasa da ƙasa, ya dace ƙasar Sin ta tsaya ga faɗaɗa bude ƙofarta ga kasashen waje, da ci gaba da amfani da kasuwannin cikin gida da na waje, don neman samun moriya tare.

Firaminista Li, ya kuma sake nanata cewa, ƙasar Sin tana samar da goyon-baya a fannin manufofi irin ɗaya, ga kamfanoni daban-daban, ciki har da na ƙasa, da masu zaman kansu, da masu jarin waje da sauransu.

Mai fassara Murtala Zhang