Babu nasara ga ’yan awaren Taiwan

Daga SAMINU HASSAN

Bisa dukkanin shaidu da dalilai na zahiri, ’yan a waren yankin Taiwan na ƙasar Sin, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar ƙasashen yamma, ba su da wani buri da ya wuce jefa Taiwan cikin yanayi na ruɗani.

Lura da hakan ne ma ya sanya mahukuntan ƙasar Sin dukufa matuka, wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da masu burin ci gaban tsibirin Taiwan, wajen shawo kan duk wasu batutuwan da suka shafi sake ɗinkuwar yankin da babban yankin ƙasar Sin cikin lumana.

Ko shakka babu, aiwatar da wannan manufa ta hanyar nacewa salon ƙasa ɗaya tsarin mulki biyu, shi ne mataki mafi dacewa na dinkuwar ƙasar Sin cikin ruwan sanyi, amma kuma duk da haka, ya kamata masu son gurgunta wannan manufa su san cewa, gwamnatin ƙasar Sin ba za ta bar duk wata kafa ta cimma nasarar ’yan a ware ba.

Bisa goyon bayan ɗaukacin al’ummun ƙasar Sin, da kudurorin MƊD masu nasaba da hakan, da ma goyon bayan sauran sassan ƙasa da ƙasa, batun dinkuwar yankin Taiwan na da tushe na dokar ƙasar Sin, da ma dokokin cuɗanyar ƙasa da ƙasa.

Kaza lika ɓangarorin da suka ki amincewa da hakan, suna ƙoƙarin ne na tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da yunƙurin gurgunta moriyar ƙasar da ikon mulkin kanta.

Sanin hakan ne kuma ya sanya gwamnatin ƙasar Sin ta shirya tsaf, domin tunkarar duk wani shiri na amfani da batun Taiwan, don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan ƙasar.

Hakan tamkar kashedi ne, da jan kunnen masu ganin za su iya keta hurumin ikon mulkin kai na ƙasar Sin. Domin kuwa Sin na da ikon amfani da dukkanin hanyoyi mafiya dacewa, na kare kai daga barazanar makiya.

Bahaushe kan ce “Idan kunne ya ji jiki ya tsira”, wato dai bayanai da mahukuntan ƙasar Sin ke fitarwa, da matakai na zahiri da gwamnatin ƙasar ke ɗauka, na tabbatar da cewa, ’yan a waren yankin Taiwan, da masu mara musu baya daga ’yan siyasar ƙasashen yamma, ba za su taba yin nasarar cimma mummunar manufar su ba!

Fassarawar Saminu Hassan