Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar Sin ta yi watsi da ra’ayin Blinken kan batun “tarkon bashi na Ƙasar Sin”

Daga CMG HAUSA

A yayin ziyarar da ya kai ƙasashen Afirka a kwanan nan, sakataren harkokin wajen ƙasar Amurka Antony Blinken, ya sake yin tsokaci kan batun “tarkon bashi na ƙasar Sin”.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya musanta wannan batu a yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa Alhamis din nan.

Yana mai cewa, batun “tarkon bashi na ƙasar Sin” karya ce da ƙasar Amurka da ƙasashen yammacin duniya suka ƙirƙira, don kauce wa nauyin da ya rataya a wuyansu, wanda ba kowa ne ya yarda da shi ba. Don haka, ya dace su bar gaskiya ta bayyana kanta.

Wang ya ce, bashin da ƙasashe masu tasowa suka ɗauki dogon lokaci suna biya, galibi ya shafi masu lamuni na kasuwancin yammacin duniya da kuma cibiyoyi daban-daban.

Bankin duniya ya yi kiyasin cewa, ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da matsakaita, za su biya bashin dala biliyan 940 a cikin shekaru bakwai masu zuwa.

Kuma daga cikin wannan adadi, kaso 67 cikin 100 ana biyansu ne ga masu ba da lamuni na kasuwanci na yammacin duniya da cibiyoyi da dama, kuɗaɗen da ake biyan gwamnatin ƙasar Sin da cibiyoyin kasuwancin ƙasar, kashi 14 ne cikin 100 kawai.

Wang ya yi nuni da cewa, ƙasar Sin ita ce ke kan gaba wajen ba da gudummawa ga ci gaba da aiwatar da shirin rage basussuka na ƙungiyar G20.

Sabanin haka, masu ba da lamuni na kasuwanci na yammacin duniya da cibiyoyi daban-daban, sun ki shiga ayyukan yafe basussuka, bisa la’akari da kare martabar lamunin da suka bayar, kuma ba su ba da gudummawar kwatankwacin na ƙasar Sin ba don sassauta nauyin bashin dake kan ƙasashe masu tasowa.

Fassarawar Ibrahim