‘Sanadin Kenan’ (1)

Daga FATIMA IBRAHIM GARBA DAN-BORNO

Cikin natsuwarsa ya nufi wurin da aka tanada domin wanke hannu a cikin ofishin nasa, ya zare safar hannunsa yana jin zuciyarsa kamar zata fito waje, saboda tsantsar ɓacin rai.

Ya rasa wacce kalma zai yi wa abokinsa amfani da ita, wajen tunatar da shi illar da ke cikin abin da yake ƙoƙarin aikatawa.

“Mus’ab shawara na zo nema a wurinka amma kake so ka caza mini ƙwaƙwalwa.”

Wanda aka kira da Mus’ab bai yi magana ba, ya ci gaba da wanke hannayensa da ruwan dettol, yana jin gefen kansa yana shirin tarwatsewa.

Dole ya nufi ma’adanen magungunansa ya ciro wani farin magani, ya valli biyu ya watsa a bakinsa tare da kora maganin da ruwa. A take ya haɗiye tare da rintse idanunsa yana karanto addu’a a can ƙasan zuciyarsa.

“Sulaiman tashi ka bar mini Ofis don Allah.” Mus’ab ya furta bayan ya nemi wuri ya zauna. Sulaiman ya saki murmushi sannan ya ce,

“Me ya sa kake son fifita Salima akan ni babban amininka? Salimar nan fa matata ce ba matarka ba.”

“Dakata dan Allah!”

Ya dakatar da shi, tare da milewa ya ɗauki rigarsa ta sama, ya kama hanyar ficewa bayan ya tattara wayoyinsa. Har ya kai bakin qofa ya juyo yana yi masa wani irin kallo, “Idan kaga dama ka kashe Salima. Kamar yadda ka ce ne, matarka ce ba matata ba. Daga ƙarshe ka ji tsoron Allah. Kamun Allah baya Sallama, baya ƙwanƙwasa ƙofa. Sannan ka tuna Salima marainiya ce. Gudun hijira da ta tsinci kanta a ciki ba ita ta ɗorawa kanta ba, Allah ne ya jarabceta da kasancewa a haka.”

Da sauri ya fice ya barshi a Ofis ɗin. Sulaiman ya ɗan yi shiru, daga bisani ya bi bayansa. A wajen mota ya same shi yana shirin buɗewa ya sha gabansa.

“Mus’ab ya kamata ka fahimceni. Tayaya zan ci gaba da zama da Salima ita ɗaya a matsayin mata? Ga ta ‘yar gudun Hijira, dan masifa ga lalurar yoyon fitsari. Haba Mus’ab yoyon fitsari fa a ke magana ba wai lalurar olsa ko kuma ciwon kai, da za ka iya shan magani yanzu anjima ka ji ka warware ba. Dan me ya sa zan yi ta zama da ita a haka? Indai maganar gaskiya kake so ya zama dole in ƙara aure, tunda ba ni na ɗora mata lalurar ba.”

Mus’ab ya yi masa wani irin kallo mai cike da tsana, “Da kyau! Ba kai ne ka ɗora mata lalurar nan ba, Allah ne ya ɗora mata. Ka cuci ‘yar mutane. Kana tunanin zaka iya haɗa taura biyu a baki ne a ya yin tauna? Ka yi kuskure Sulaiman.”

Da hanzari Sulaiman ya dube shi cike da mamaki ya ce, “Ma cuci ‘yar mutane fa ka ce? Ta ya ya zan zama sanadin waɗannan masifun da suke tare da ita? Wa ya sani ma, ko har cutar nan mai karya garkuwan jiki ta kwaso, a wajen yawon su na gudun hijira. Wallahi Alhaji ya cuceni, ya cuci rayuwata. Ya rasa da nakasasshiyar da zai haɗa ni sai wacce ta ƙare rayuwarta a ƙarƙashin gada.”

Mus’ab ya kasa ko da ƙwaƙƙwaran motsi, sai kallon Sulaiman yake, kamar yau ya fara ganinsa. Tunani barkatai suka cinkushe masa ƙwaƙwalwa.

Da sauri ya ture shi gefe ya shige motarsa, a ya yin da ya tashi motar da a guje ya bar harabar asibitin cike da saƙe-saƙe.

‘Yarinya ƙarama tana fuskantar barazana a dalilin faruwar ƙaddararta. Ya kamata a yanzu ta ɗanɗani farin ciki ko yayane. Ta yaya zan iya canza maka rayuwa Sulaiman?’ Mus’ab ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.

So yake ya daina tunanin abin da ya shafi rayuwar Salima bare kuma har akai ga shiga hurumin da babu ruwansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *