Masu shirya finafinai ba sa daraja gudunmawar marubuta – Ummi Zee Aflam

“Da alƙalamin marubuci kowanne ɗan fim ke taka rawa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Marubuta mutane ne masu ɗimbin baiwa, da suka fito daga ɓangarorin rayuwa daban daban. Babu wani fage da za ka tarar babu marubuci a ciki. Bilhasali ma marubuta su ne malaman al’umma, domin duk wani fage na ilimintarwa sai da marubuta suka ɓata hankalin dare, sannan suka tsara rubutun yadda za a isar da shi ga al’umma. A ɓangaren rubutun adabi, akwai marubuta da ke ba da gudunmawa wajen bunƙasa rubutun zube da na wasan kwaikwayo, wanda masu shirya finafinai ke ɗauka don tsara yadda za a fitar da labarin a aikace, domin koyar da wasu darussan rayuwa cikin yanayi na hannunka mai sanda. A cikin matasan marubuta masu ba da gudunmawa wajen bunƙasa rubutun adabin Hausa akwai Malama Ummu-Abiha Tasi’u, wacce aka fi sani da Ummi Zee Aflam, wacce bayan kasancewar ta ma’aikaciyar jinya, Ummi marubuciya ce da ke da kishi wajen kare martabar marubuta da rayuwar ýaýa mata. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, marubuciyar ta bayyana damuwarta yadda a cewar ta masu shirya finafinai ke ci da gumin marubuta. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.

BLUEPRINT MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
UMMU-ABIHA: Sunana Ummi Tasiu, wacce a ka fi sani da Ummu-Abiha, ko kuma ‘Yargote. Ni ýar Jihar Kano ce. An haife ni a ƙaramar Hukumar Tudun Wada Ɗankadai. Ni ma’aikaciyar lafiya ce, ina aiki a asibitin ƙwararru ta Murtala Mohammed da ke Kano. Sannan ni ýar jarida ce mai rubuce rubuce a yanar gizo wato blogger, Ina da shafina mai suna Northwest24.com, kuma Ina harkar haɗa man gyaran jiki na mata, da su Humra da turaren wuta na jiki da na kaya har da na ɗaki, da dai sauransu, ƙarƙashin sunan kamfanina Northwest Scent Palace.

Yaya rayuwarki ta kasance a harkar karatu?
Na yi karatun firamare na a Model Primary School Tudun Wada. Sannan kuma na wuce makarantar sakandiren gwamnati ta ýan mata ta Arabiyya da ke Tudun Wada, na fara da jeka ka dawo, sannan daga baya na koma kwana, duk a cikin makarantar. Da yake Ina da sha’awar karatun ilimin kimiyya sai Allah ya taimake ni na samu shiga makarantar koyar da ilimin lafiya ta ‘School of Health Technology’ Kano, inda na samu ilimina a matakin Diploma ɓangaren kula da lafiyar al’umma, wato ‘Community Health’. A yanzu haka ina ƙoƙarin juyawa zuwa digiri, in Allah ya so.

Gaya mana yadda ki ka fara samun kanki a matsayin marubuciya?
Tun Ina aji uku na ƙaramar sakandire wato JSS 3, akwai wani malaminmu da ke koyar da mu darasin kimiyya na ‘Integrated Science’ mai suna Yaro Jinjiri, shi ne ya fara kwaɗaitar da ni rubutu ganin yadda nake da sha’awar karance-karance. Ya kawo mana misalan makarantu da suka samu cigaba, ta hanyar wallafa littafi mallakin makarantar. To, a nan ya yi alƙawarin duk wacce ko waɗanda suka rubuta littafi a cikinmu, zai ɗauki nauyin buga shi. Tun daga nan na ƙuduri niyyar fara rubuta littafi.

A wacce shekara ki ka fara rubutu, kuma da wanne littafi?
Na fara rubutu ne a 2009, sannan na fara da littafi mai suna ‘Hayaniya’ (littafi ne na labarin yaƙi), sai dai kash, Ina cikin rubutun littafin ban gama ba, ƙanina ya yaga min shi. Sai na sake ƙoƙarin rubuta wani littafin a ɓangaren soyayya, na sa masa suna ‘Da Wa Zan Ji?’ Shi ma dai ban gama ba, muka fara jarrabawar ƙarshen zangon karatu na biyu, a makaranta.
To, kuma Ina tsaka da ci gaban rubutun, a ka yi wa malamin canjin wajen aiki zuwa wani gari. Sai a shekarar 2018, sannan zan ce na zama cikakkiyar marubuciya, da taimakon wasu marubuta da suka tallafa min da shawarwari, ciki kuwa har da mahaifina. Akwai irin su Hamza Dawaki, Bamai Dabuwa, Ado Ahmad Gidan Dabino, Al-Mustapha Adam, Zulaihat Rano da sauran marubuta da muke hulɗa tare yau da gobe. Godiya ta gare su ba za ta kare ba.

Gaya mana adadin yawan rubutun da ki ka yi na littattafai?
Na rubuta littattafan aƙalla kamar guda shida. A cikin su akwai ‘Da Wa Zan Ji?’ ‘Dabaibayi’, ‘Munafikar Mata’, ‘Sailuba’, ‘Mijin Gado’. Sai wanda nake kan rubutawa a yanzu ‘Ƙawalwalniya’ wanda kuma nake da burin buga shi a matsayin littafi na takarda, idan Allah ya ba ni iko.

Wanne ɓangare ki ka fi mayar da hankali a kansa a rubuce-rubucenki?
Na fi mayar da hankalina ga rayuwar da mu ka tsinci kanmu a yanzu. Musamman ma a ɓangaren taɓarɓarewar tarbiyya da kare mutuncin rayuwar ýaýa mata.

Yaya mu’amalar ki take da masu bibiyar littattafanki, kuma wanne abu ne suka yi miki da ya tsaya miki a rai, na farin ciki ko akasin haka?
Gaskiya akwai kyakkyawar mu’amala a tsakanina da masu karanta littattafaina, domin kuwa har kyaututtuka sukan yi min, domin faranta min rai. Sannan farin ciki mafi girma da ba zan iya mantawa da su ba, wasun su sun girme ni, amma haka su ke girmama ni, duk da cewar ba su taɓa ganin ko da hotona ba.

A kan samu wasu marubutan adabi da suke komawa rubutun fim, shin ke ma kina da ra’ayin rubutun fim, kuma wacce riba ki ke samu?
E, a matsayina ta marubuciya, Ina da ra’ayin rubutun fim. Saboda akwai wani sabon kamfani da aka buɗe a shekarar 2019 sun nemi da na riƙa rubuta musu labarin fim wato ‘script’ don su riƙa saya. Amma sai Allah ya sa ba mu daidaita ba, saboda yadda suka ce za su riƙa biyana. Gaskiya ni ban yarda da tsarin da suke so ba, don na lura kura ce da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Babu shakka masu harkar finafinai suna barin marubuta a baya. Za ka ga marubuci ya dage ya taƙarƙare ya yi rubutu, amma kuɗin da za a sayi labarin, ba ya kai kuɗin da a ke biyan ‘yan wasa.

Ba a yi wa marubuci kyakkyawar sallama, sai Ina ganin kamar da gangan ake dakushe ɗaukakarsa. Sai ka ga yarinya ko saurayi ya shigo harkar fim ya yi suna a lokaci kaɗan, amma marubuci sai ya kai shekara goma yana rubutu kafin duniya ta san shi. Shi ɗin ma sai ta kama ake sanin sa. Alhalin suna mantawa da alƙalamin marubuci kowanne ɗan fim yake ta ka rawa. Da alƙalamin marubuci ita kanta duniyar ta ke juyawa a yanzu haka.

Yaya ki ke ganin marubuta za su kare martabar su da darajar aikinsu a wajen masu shirya finafinai?
Marubuci ya yarda a ransa cewar sai da shi fim zai ginu, idan babu shi to babu fim, dole sai ya yarda da hakan. Haka ne zai ba shi ƙwarin gwiwar ya sayar da rubutunsa da daraja, kar neman ɗaukaka ya sa, ya dinga sayar da rubutunsa kara zube, domin neman suna. Hakan na iya janyo mishi ba wan ba ƙanin. Kuma ba za a riƙa ɗaukar rubutunsa da mutunci yadda ya kamata ba.

Su kuma ma su shirya fina-finai, ya kamata su sani cewar da bazar marubuci suke taka rawa, ba don shi ba da babu su a fagen finafinai, kuma da duniya ma ba za ta san su ba. Don fim ya dogara ne da labarin da za a tsara, ko da kuwa ba za a ce uffan a ciki ba. Dan haka dole ne su riƙa sayen labari a farashi mai daraja. Da bai wa marubuci haƙƙinsa na wanda ya rubuta.

Su ma kuma marubuta har wa yau su zama masu yin rubutu cikin hikima, su riƙa ƙirƙirar sabon labari, wanda ba a san shi ba, sannan su yi ƙoƙarin ganin sun cika alƙawari iya wa’adin da ya ɗauka musu. Hakan zai sa mu zamo masu kwarjini, kuma hakan zai qara sanya darajar mu ta ɗaukaka. Saboda duk wani abu da a ka ce harka ce ta kasuwanci, ana buƙatar cika alƙawari. Kuma duk mai cika alƙawari, darajarsa, da kimarsa na ƙara yawaita a idanuwan mutane. Lallai marubuci ya kula duk lokacin da zai rubuta labari, ya kasance labarin sabon labari ne, wanda mai karatu ko mai kallo bai san shi ba, hakan ba zai sa ya gajiya wajen kallon fim din ba.

To, ai wasu na ganin su ma marubutan musamman na online kara zube suke fitar da littafin su babu wani abu da suke samu, ke kin taɓa samun wani alheri ta dalilin rubutu?
Gaskiya ban yarda da wannan batun ba, babu marubucin da ya san darajar basirar sa da alƙalaminsa, da zai nuna ko oho da abin da yake yi ba. Na san akwai masu rubutun kyauta da kuma littafin kuɗi. Kowanne kuma ana ware shi tare da bambanta yadda za a saye shi ko biyan kuɗi ta banki. Nima haka nake yin na wa kuma Ina kan samun alheri a yanzu haka.
Marubuta na amfani da hanyoyi daban daban kamar su manhajar wattpad, Arewa Books ko Okada Books da sauran su, marubuta na sayar da littattafansu a nan. Kuma su masu karatu a ko da yaushe suna ƙoƙarin ganin ba su rasa ko daidai da kalma ɗaya ba ne a littafi, don haka suke rige-rigen sayen littattafan da muke rubutawa.

Ta yaya ƙungiyoyin marubutan online za su kawo sauyi ga yadda suke rubuce rubucen su?
Ni a tawa fahimtar, tsoron Allah shi ne kan gaba. A daure a yi rubutun da zai fadakar da al’umma, wanda mutane za su amfana da shi. Sannan a guji amfani da kalmomin cin zarafi ga wata ƙabila, ko addini, ko savawa tarbiyya da al’adun mu ta Musulunci. A guji rubuta kalmomin batsa. Ina ganin ta haka ne za a iya kawo gyara. Mu riqa yin rubutun da zai kawo canji a yanayin zamantakewar al’umma da muhallinsu ba kawai don nishaɗi ba. Yanzu haka a wasu ƙasashen da suka samu cigaba, marubuta na daga cikin waɗanda suka ba da gagarumar gudunmawa ta hanyar rubuce rubuce da suka yi tasiri sosai, saboda cigaban zamani.

Gaya mana lokacin da ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Na fi sha’awar rubutu a lokacin da na tashi daga barci. Sannan kuma Ina sha’awar rubutu a gurin da babu hayaniya, duk da cewar daman ni ba mai son hayaniya ba ce. A lokacin ne nake iya zuba rubutuna ba ƙaƙƙautawa.

Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?
Wani hanin ga Allah, sai kuma ɗan hakin da ka raina…

Mun gode.
Ni ce da godiya.