Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Libya ta musanta duk wani zargi na cewa suna da hannu a kan abinda ya samu Super Eagles na Nijeriya.
Jaridar Blueprint Manhaja ta samu rahoton cewa ‘yan wasan Nijeriya sun shafe awanni a filin jirgi a ƙasar ba a bar su sun fita ba.
Bayan nasarar da Nijeriya ta samu kan Libya a Uyo, Jihar Akwa Ibom, a ranar Juma’a, an shirya wasan zagaye na biyu na neman gurbin AFCON 2025 a Benghazi, Libya, a ranar Talata.
Kafin wasan, tawagar Nijeriya ta tafi Benghazi ta hanyar jirgin sama.
Sai dai, jirgin ya canza hanya daga inda aka nufa kimanin awa daya kafin isa bisa wasu dalilai da ba a san meyasa ba.
‘Yan wasan Nijeriya sun sauka a filin jirgin sama na Al Abraq, wanda ake amfani da shi kawai don ayyukan hajji a maimakon birnin Benghazi.
Bayan sauka, NFF ta yi shirye-shiryen zuwa wurin wasan da kanta saboda rashin jami’an Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Libya.
Duk da haka, jami’an filin jirgin sama ba su bar motar da hukumar NFF tai haya ta shigo filin jirgin sama ba.
Bayan wannan al’amari, Super Eagles sun yanke shawarar cewa ba za su buga wasan ba, sai dai su koma gida.
A yayin da LFF ta mayar da martani a wata sanarwa a ranar Litinin, ta ambaci ƙa’idojin kula da zirga-zirgan jiragen sama, a matsayin dalilai da za su iya shafar tafiye-tafiyen jiragen sama.
Hakanan sun ce an sami irin wannan al’amari lokacin da ‘yan wasan su suka tafi Uyo, Nijeriya, don wasan zagaye na farko.
Sanarwar da aka fitar a shafin X ta ce: “Mun matuƙar damuwa da rahotannin da suka shafi canjin hanyar jirgin tawagar Ƙwallon kafa ta Nijeriya.
Duk da cewa muna nadamar duk wani rashin jin daɗi da hakan ya haifar, yana da muhimmanci a fahimci cewa irin wannan abubuwa na iya faruwa saboda ƙa’idojin kula da zirga-zirgan jiragen sama.
“Babu hujja da za ta tabbatar da cewa rundunar tsaro ta Libya ko Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Libya sun yi wannan lamari da gangan. Wannan lamari bai dace da ɗabi’un mu da ƙa’idojin mu ba.
“Muna musanta duk wani zargin da ke nuna cewa an yi laifi a wannan lamari. Yana da muhimmanci a jaddada cewa a makon da ya gabata, tawagar Ƙwallon ƙafa ta mu ma ta fuskanci manyan ƙalubale bayan isowarmu Nijeriya don wasa na uku na neman gurbin gasar cin kofin Afrika.
“A Libya, muna alfahari da kyautatawa da kyakkyawar tarba. Mun kasance muna fifita kulawa da dukkan tawagogin da ke ziyara, ciki har da ‘yan uwannanmu na Afrika da sauran wakilan duniya, da girmamawa da daraja da suka dace.