ZASIEC ta tsaida 16 ga Nuwamba don zaɓen ƙananan hukumomin Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Zamfara ZASIEC, ta sanya ranar 16 ga watan Nuwamba domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

Shugaban hukumar na jiha, Alh. Bala Aliyu Gusau ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ofishin sa a yau Litinin.

A cewarsa, hukumar zaɓen za ta gudanar da zaɓen ne bisa doka mai lamba 4, ta hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar wadda ta bai wa hukumar damar gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin da kansiloli a faɗin ƙananan hukumomi 14 da ke jihar.

Gusau ya ce za a fara siyar da fom da cikewa tare da mai do wa ga hukumar daga 25 ga Oktoba zuwa 1 ga Nuwamba a tsakanin ‘yan takarar baki ɗaya.

Hakazalika ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen a jihar.

“Mun kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi 14 kuma muna fatan za a gudanar da zaɓe a jihar ba tare da samun matsala ba. Yace

By ukarofi