Yanzu-yanzu: Jirgin Super Eagles ya sauka a Nijeriya bayan wahalar da suka sha a Libya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Tawagar Super Eagles sun iso Nijeriya bayan wahalar da suka sha a Libiya domin buga wasan cancantar shiga gasar cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2025 (AFCON).

‘Yan wasa da jami’an tawagar sun maƙale a filin jirgin sama na Libiya har tsawon sa’o’i 13 kafin wasan da aka shirya za a buga ranar Talata. Hotunan tawagar suna barci a kan kujerun filin jirgin sun bazu sosai a safiyar Litinin, wanda ya jawo suka daga ‘yan Nijeriya da dama.

Amma sa’o’i kaɗan bayan haka, tawagar ta sauka a Nijeriya bayan hukumomin Libiya sun ba da izinin jirginsu ya tashi.

By ukarofi