MAKAMASHI: Matsaloli ƙare, an gano bakin zaren

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Watan Oktoba ya zama watan rahama ga ’yan Najeriya, watan wanda ɗaya gare shi a shekara ta 1960 ƙasa ta wayi gari a matsayin ’yantacciyar ƙasa da samu daga ƙasar mulkin mallaka ta Birtaniya, wato ƙasar Ingila bayan ta kwashe sama da shekaru 100 ta na mulkar ta da kuma kwasar dukiyar ƙasa tun daga amfanin gona da ma’adanai da kuma makamashin kwal, wanda a lokacin yake ƙanshin ɗan goma a kasuwannin duniya.

Bayan shekaru goma sha uku kacal da tafiyar su, suka dawo cikin hikima da sabbin dabaru bayan haɗin kai da suka samu daga sauran ƙasashen yammacin Turai, Kamar faransa da Jamus da Portugal da Italiya da Babbar ƙasar da suka raina, wato amurka (U.S.A) suka shiga kwasar ɗan yan man fetur (Crude Oil) a cikin mu suna basu kamasho da la’ada  waɗan da suma suka samar da ‘yan kasuwar tsaye da kuma ‘yan kasuwar bayan Fagge.

Lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya soke wannan kamasho da la’ada da suke kira ‘Subsidy’, a ranar rantsar da shi a watan mayu na shekara ta 2023, tun daga suka kuwa sako zakuna da karaye baki buɗe a kasuwannin hatsi da kayan masaruhi inda ‘yan najeriya suka tarwatse, babu Abinci bau lafiya sama da kasha tamanin suka faɗa tarkon talauci da ƙaƙanakayi Al’amura da suke da alaƙa da tsaro da futuntunu ta fuskar ƙabilanci da bambancin addini da cin hanci da rashawa da kuma sama da gaskiya a tsakanin al’umma da kuma kiraye – kiraye irin ya kama gaban sa.

Cikin hukuncin kubbani watan da ya gabata na satumba sai ga labara matatar man fetur ta mashahurin attajiri Aliko ɗangote ta fara ƙarɓar ɗanyan man fetur daga NNPCL a farashin nair domin tacewa, kuma zatayi kasuwancisa shima a farashin naira, ‘yan ƙasa saunyi farin ciki mutuƙa da gaske. A nan nne, a zauren wani Alƙali na Kotun ɗaukaka ƙara ta Addinin musulunci da yayi ritaya a shekara ta 2015, kuma ya buɗe makarantar Zaure inda yake koyar da fannoni na Ilimi masu yawan gaske.

A nan ne da yaji wannan Magana ta matatar man fetur ta ɗangote sai yace da ɗalibansa, “Matsalolin Najeriya, sun zo ƙarshe domin kuwa an gano bakin zaren,” cikin sharhin wannan Magana cutar da cewa, likita zai iya baka maganin cutar da ta addabe ka da zarar ya fahimci me yake damun ka. Matatun man fetur na ƙasa basa ayki sai wani yayi kuma hukuma ta yarda da ingancin sa.

Al’umma sai ta karɓa ta sha komai tsadarsa, Kamar mai shan magani ne ɗacin sa, domin kuwa waraka ake nema. Tun da mai ya samu a cikin gida sai kuma anemi hanyoyin sauƙaƙa farashi. Malam yace, sauƙaƙa farashi akwai hanyoyi uku, na farko yawan kaya a kasuwa wanda yafi  ƙarfin mabuƙata. Hakan kuwa zai samu ta bawa mutane da ma da gwamnatoci su shiga sana’ar tace ɗanyan man fetur akalla bibiyu a duk yankunan da ake da su, kunga za a sami guda goma sha biyu  ke nan.

Baya ga haka matatun da ake kira “Haramtattu” a yi musu iyaye, ma’ana ahartasu, suma abasu dama su shiga tace men fetur da dangogin su, man fetur ina tabbatar muku zai zama kamar “Oure water” da ruwan jarka (Roba) a birninAbuja, inji mala. Kuma malam ya ƙara da cewa kafin shekara ta 2030 sherar da majalisar ɗinkin Duniya  ta sanya ƙasashe na ƙungiyar ‘OPEC, Wanda har da Najeriya da ire – iren su dasu fito da mafita dangane da harkokin tattalin arzikin su saboda matsalolin ɗumamar yanayi da muke ganinsu a zahiri yanzu.

Mu na da masaniya tsare – tsaren da duniya take dashi kan makamashi nan da shekara ta2050 musamman kan man fetur da gas zasu zama Tarihi kamar yadda tagomashin da makamashin kwal (Coal) ya samu daga 1930 zuwa 1950 a faɗin duniya. A nan gida Najeriya a tuntuɓi mutanan Enugu da abakaliki da lafia a jahohin Enugu da Nassarawa da kuma Plateu. ‘Yan Najeriya da aka Haifa a shekarun 1980, 90 da kuma 2000 musamman da suke kan hanyar doga (Jirgin ƙasa) daga Legas zuwa Ibadan Tafi – Tafi zuwa Kaduna zuwa Kano har a kai Nguru a jahar Yobe da kuma Gusau da Kausa Namoda a Jahar Zamfara. Haka daga Enugu zuwa Plateu tafi tafi zuwa Maiduguri waye ya san gwari  kan Jirgin ƙasa da ke tuƙa taragwai da suke ɗaukar tan – tan na dubban kayayyakin amfanin gona da ma’adanai irinsu kuza, bakin ƙarfe (iron ore), Tantalite  gorar ruwa, kai ma’adanai sun 20 a wancan Lokacin, amma yanzu su na kundayen tarihi.

Tarihi zai ba wa al’umma mai zuwa nan gaba, cewa makamashin man fetur da gas da sauran dangoginsa sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar bil – Adama wasu cikin daɗi da wal wala wasu kuwa cikin fatara da Talauci kamar ‘Yan Najeriya duk da cewa suna Farko – Farko Wajan samar da wannan makamashi a doran Duniya, amma saboda siyasar kashin dankali da kuma annoban cin hancii a rashawa  da kuma ridda ciki da babakere da dukiyar daga  wasu ’yan kalilan da ake kira da ‘yan takarda – ‘elite’.

Tsari mai kyau da shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai fito daga al’umma duniya na falsa duk wanda ya taɓa dukiyar Nijeriya  ko mai ƙanƙanta ta yayata shi, duk inda shiga a faɗin duniya ta  yi masa lamba barawon najeriya kuyi taka tsantsan  da shi. Koda kuwa ta hadin baki. Mu na fata za a gaggauta wannan doka kuma a  ƙara da masu tsauwala farashi  domin cin kazamar riba a wasu Muhimman abubuwa da suke da alaka kai tsaye da al’ummar ƙasa. Duk wanda aka ji yana sukar  wannan doka a sanya shi acikin masu yi wa ƙasa zagon ƙasa.

By ukarofi