Litar fetur sai yadda hali ya yi

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Yanzu dai an haƙiƙance tsadar litar man fetur sai yadda hali ya yi a Nijeriya tun da gaba ɗaya a hukumance gwamnati ta miƙa ragamar kasuwancin kamfanin fetur NNPC a hannun ‘yan kasuwa. Ka ga ba sauran wanda za a yi wa ƙorafi don an ga litar fetur ta yi tsada. Dama an ɗauka cewa lamarin zai inganta bayan ganin gidajen mai a jihohi na sayar da fetur kan Naira 190 har ma an samu inda su ka sayar Naira 225 maimakon Naira 165 da a ka sani.

Gaskiya ni ma sai da na lura na gane ashe a tsakiyar Abuja ne a kan sayar da man Naira 165 na wani lokaci gabanin yanzu da litar ta cilla sama. Wasu dalilai da ke tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa su ka bayyana kan cewa a kan biya tallafi s cikin Abuja ne amma sauran sassa an zare dukkan tallafin ɓoyen.

Ta kan yiwu gwamnati ta yi hakan ne don rufe bakin ‘yan boko da manyan masu ƙorafi da ke birane don kar su tada jijiyar wuya a samu ruɗani a ƙasa. Ta ƙarƙashin ƙasa gwamnati ta zare hannun ta daga dukkan tallafin fetur ta bar jama’a su nemi kuɗi su saya da ɗan karen tsada. Ai lamarin ya zama kasuwa ta yi halin ta ne don wasu ƙa’idoji na a sayar daga Naira kaza zuwa kaza ba lalle ya tafi a hakan ba. Kuma barin fetur ɗin na Abuja a lokacin da wannan tallafin ya sa kullum sai dogayen layuka da kan sa wasu su kwana su na sa ran samun man kan farashi mai rangwame.

Yau fa a ke yin ta don son samu man mai tsadar gaske ya wadata a ko ina. To gudajen mai in sun zama tamkar yara masu riƙe jarka da tiyo a gefen titi don sun sauya zuwa ‘yan baƙar kasuwa masu lasin. Ba wani abun alfahari ko murna ba ne don mutum ya shiga gudan man ‘yan baƙar kasuwa ya saya ba dogon layi. Aljihun mutum zai gaya ma sa labarin ɓoye. Komai yanzu ya bayyana gari ya waye na babban ƙalubalen da ya shigo Nijeriya. Ƙasar ta ƙara zaunawa daram kan muqamin ta na jari hujja a ƙasashe masu tasowa inda talakawa ke kara talaucewa masu kuɗi ke ƙara kudancewa.

A ƙasashen da jari hujjar su ke da imani a kan samu wasu abubuwan da ba sa gagarar talaka samu kamar ruwan sha mai tsabta, wutar lantarki, burodi da sauran su. Zan zayyana waɗannan ƙasashe da ‘yan farar jari hujja amma a ƙasar jari hujja mai duhu don ba na son tsawatawa na ce baƙar jari hujja akwai bambanci tsakanin iskar da talaka ya ke shaka da wacce ‘yan jari hujja ke shaka. Gargadin shi ne matuƙar dai duk a ƙasa ɗaya a ke zama ta wataran dole a haɗe a wasu lamur da su ka zama dole. Wahala tamkar hantsi ta ke leka gidan kowa. Da zarar damuwa ta kai iya wuya dole mutane su yi ƙorafi don samun sauƙi.

Babban ƙalubalen ƙaruwar farashin man fetur shi ne tashin gauron zaɓi na farashin muhimman kayan masarufi. Ko gabanin ma tashin farashin litar zuwa wannan yanayi mai ban tsoro an samu tashin farashi mai tsanani inda mutane ba sa iya shiga kasuwa su sayi abun da su ka saba saya a baya. Kusan duk abun da ka taba sai ka ji an ce ya ƙara kuɗi don haka mai sayan biyu sai ya sayi ɗaya mai sayen ɗaya kuma sai ya ce a ba shi rabi ya jalabta.

Bayan lashe zaven shugaba Buhari na shekara ta 2015 gwamnatin sa ta ƙara farashin litar fetur daga Naira 87 zuwa Naira 145. Saboda sabuwar gwamnati ce da ta hau mulki bayan doguwar gwagwarmaya ya sa mutane su ka amince da ƙarin da juyawa ƙungiyar ƙwadago baya da ke son a tafi yajin aiki. Akasarin mutane sun yayata cewa Allah ya ba su kuɗin saya don sun yi na’am da cewa gwamnatin na da manufa mai kyau kuma ba za ta ɗau wani mataki da zai cutar da su.

Hakan ya sa mutane sun gwale ƙungiyar ƙwadago ta hanyar kin biye ma ta a shiga yajin aiki. Ƙungiyar ƙwadago ta yi yunƙurin yajin aiki har da zanga-zanga amma rashin goyon baya ya sa ala tilas ta janye yajin kuma tun a wancan karo ba ta sake wani tasiri mai ƙarfi na yajin aiki ko wata barazana ba.

Ƙarshe ma an shiga zargin ƙungiyar ƙwadagon ne da yin ƙumbiya-ƙumbiya a lamarin yajin aiki musamman a zamanin Obasanjo. In da a shekarun baya ne a ka samu wannan yanayin bashakka da zuwa yanzu an fara samun shirin zanga-zanga da yajin aiki. Masu nuna damuwa mai tsananin ma na addu’a ne cewa Allah ya kawowa Nijeriya shugabanni na gari a 2023. Shin in shugabanni na gari su ka zo da wataƙila sun fi waɗanda ke gado adalci za su dawo da tallafin fetur ɗin ne ko kuwa a’a?.

Abun lura dai a nan mutane sun hango tsadar rayuwa kuma da alamu sun samu sanyin gwiwa ga shugabannin da su ka yi amanna cewa za su ɗauki matakan sama mu su sauƙin rayuwa. An samu dogon lokaci gabanin 2015 ’yan adawa ƙarƙashin Muhammadu Buhari na caccakar tsohuwar gwamnatin PDP da kawo ƙuncin rayuwa ciki kuwa har da tsadar man fetur da kashe kuɗi kan ba da tallafi inda su ka ce wasu ke sace kuɗin. Akwai lokacin da shugaba Buhari ya yi wani jawabi ya na nuna al’ajabin abun da a ke nufi da tallafin man fetur don bai yarda da shi ba.

Ya ce ya na son a zo a gamsar da shi kan tallafin. Bayan nasarar hawa mulki sai a ka gano daga bisani ashe ita ma gwamnatin shugaba Buharin za ta cigaba da ba da tallafin. Ina ganin in ban da wannan makwan ba a tava dakatar da ba da tallafin fetur ko a na amfani da shi ta hanyar da ta dace ko sacewa a ke yi sai bincike ne zai nuna. Kuma har yau ɗin nan ’yan kasuwar fetur na bin gwamnati bashin jigbin kuɗi na tallafin fetur. Kun ga kenan ba wani sauyi a ka samu ban a janye tallafin a gwamnatin Buhari har zuwa shekararta, ta karshe kan mulki. Idan wannan shi ne gaskiyar janye tallafi to za a fahimci amfanin tallafin ko akasin haka.

Sannan ya zama mai muhimmanci gwamnati ta fito karara ta ba da haƙurin yadda a ka riƙa jeka-ka-dawo kan batun an janye tallfin ko har yanzu ya na nan. A kan yaɗa wata manufa cewa in an janye tallafin za a tura kuɗin zuwa wasu ayyukan sauƙaƙa wa al’umma ƙuncin rayuwa. Jikin mutane zai gaya mu su ko sun samu sauƙin ko ba haka ba ne.

A ƙarshe dai gwamnatin Nijeriya ta miqa kamfanin man fetur NNPC hannun ’yan kasuwa ko ya zama mai zaman kansa kamar yadda kamfanoni masu zaman kansu da a kan zuba jari su ke.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da miƙa kamfanin ga ’yan kasuwa a ɗakin taro na fadar Aso Rock, inda ya yaye ƙyallen tabbatar da hakan yayin da shugaban kamfanin Mele Kyari Kolo ke tsaye ya na shaida hakan.

Muhammadu Buhari ya ce, yanzu kamfanin na da masu kula da hannun jarin sa wajen miliyan 200 kuma hakan zai kawo ƙarshen cin hanci da rashawa da kamfanin ya yi ta fama da shi a baya.

Matakin ya nuna tsame hannun gwamnati kai tsaye ga lamarin kamfanin inda yanzu ’yan kasuwa da ke da jari ba za su bari a murde mu su kuɗi ba. Dama ai an sha cewa gwamnati ba za ta iya tafiyar da kamfani ya samar da ribar da a ke so ba don wasu za su iya amfani da matsayin su a gwamnati wajen wawurar dukiyar kamfanin don mallakar gwamnati ce da a ke yi wa kirari da ‘ba ki son kuɗi sai mulki’.

Illar ta zahiri ita ce tashin gauron zaɓin farashin man fetur da hakan zai cilla farashin kayan masarufi sama zuwa ɗan karen tsada. Kama daga lamuran sufuri, muhimman kayan abinci da ma kuɗin makarantar yara zai tashi. Ba yau a ka fara samun irin wannan ƙalubalen ba matuƙar a ka samu cillawar farashin litar fetur. Ba ma sai an danganta tsadar kan dala ba, yanzu kai tsaye muhimman kayan na masarufi da a kan yi jigilarsu a mota zuwa dogon zango daga inda a ke sarrafa su za su yi tsada.

Kammalawa;

Abu mai muhimmanci ga jama’ar ƙasa shi ne amfani da ilimi wajen gudanar da rayuwar ta yau da kullum wato misali maimakon ɓugewa da wutar lantarki daga kamfanin wuta sai a fara bunƙasa fasahar samar da wuta daga hasken rana. Hakanan ya dace shi kan sa makamashi a samu hanyar amfani da dusar katako da risho mai ma’ana don samun makamashin ba tare da ƙona itatuwa da yawa ba don su ma sun a taimakawa wajen rage ƙuncin rayuwa. Duk wata fasaha ta samar da kayan aiki na rayuwar yau da kullum cikin sauqi ya dace a bunƙasa ta. Hakanan a rage ciki ko cin abinci har a ƙoshi a yi ƙit ɗin nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *