2023: Zaɓen Shettima a matsayin mataimakin Tinubu daidai ne – NPCF

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa farar dabara ce zaɓen da Bola Tinubu ya yi wa Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a babban zaɓen 2023.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da shugaban ƙungiyar kansiloli na ƙasa (NPCF), Honarabul Muslihu Yusuf Ali, mai wakiltar gundumar Gurungawa, Kumbotso, Jihar Kano ya fitar a ranar Asabar.

Ali ya ce, nasarar da Tinubu ya samu na zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa na APC na 2023, abu ne da babu makawa.

Ya ce dukkanin ‘yan takarar sauran jam’iyyu babu wanda zai iya karawa da Tinubu saboda ya yi musu fintinkau a fagen siyasa, kai tsaye ko a kaikaice.

Ya ce, Tinubu mutum ne wanda ya bada gudunmawarsa ga haɗin kai da kuma cigaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa, tunanin da jam’iyyun hamayya ke da shi na cewa bataun takarar musulmi biyu (Muslim-Muslim ticket) gazawa ce ga APC, kuma cewa hakan ba zai samu karɓuwa ba a wajen Kiristocin Arewa, amma sun manta cewa lamarin shugabancin ba ya la’akari da komai face cancanta, daidaito, adalci da kuma juriya.