Fifita ilimin boko a kan na addini

Duniya ina zaki damu? A haƙiƙanin gaskiya wannan rayuwa mun kai wani mataki da iyaye da kansu ke nuna wa ’ya’yansu duniya ta fi lahira. Wannan kuma ba ƙaramin ƙalubale ba ne gare mu Musulmi.

Sakamakon hakan, ya sa yara za su taso da sangarta, rashin tarbiyya, ga rashin kula da addinin Allah. A haka kuma za ku ga ko sallah ma ba ta dame su ba, kuma ba su ɗauki iyayensu a bakin komai ba. Me ya jawo hakan? A wani ɓangaren kuma ku dubi amfanin ilimantar da ‘ya mace.

A wannan yanayin da muke ciki kashi casa’in 90% na iyaye cikin ɗari sun fi fifita karatun boko a kan na addini, idan ’ya’yansu suka tafi makaranta tun bakwai ba su dawowa sai yamma, wasu sai ƙarfe shida wasu ƙarfe biyar da ƙyar ake tura yara islamiyya su yi awa ɗaya, wata rana ma sai a ce kwanta abinku kun gaji. Ba ma a nan gizo ke saƙar ba sai ya zama ko karatun sallah ba su iya ba balle aibatun sauran haƙƙoƙin Allah da kuma addini, a haka dai za su taso suna gama karatunsu na sakandare za su tafi jami’a inda kwata-kwatama zancen karatun addini ya ƙare a haka, shikenan ba wan ba ƙanin.

Saboda Allah iyaye mai za mu ce wa Allah a ranar alƙiyama, muna mantawa da amanar da ya ba mu a kan ’ya’yanmu. Sannan a haka ake tura yara ƙasashen waje don neman ilimin boko ba tare da an yarda da ingancin iliminsu na addini ba, da sun dawo a musu aure a ba su aiki, shikenan rayuwarsu ta ginu cikin tavewa a haka sai su yi ta aikata varna yadda su ke so a doran ƙasa.

Ina mai jawo hankalin iyaye da su ji tsoron Allah, wallahi akwai ranar za ta zo da za su ba da bayani a kan yadda suka tarbiyyantar da ’ya’yansu domin wannan matsala tana taimakawa wajen zinace-zinace da ɓarna a cikin al’umma tun da yaran ba su ma san kan su ba balle su yi tunanin tsoron Allah, wa’iyazu billah. Allah shirya mana zuri’a, ya sa masu wannan mummunar ɗabi’a su gyara, Ameen.

Wassalm. Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.