Littafin koyon salatin Annabi cikin sauƙi

Daga IBRAHIM SHEME
 
LITTAFI: Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam: Matsayinsa Da Fa’idojinsa Da Sigoginsa
MARUBUCIYA: Hajiya Hajara Muhammad Kabir
KANFANIN WALLAFA: Goshi Publishers Limited, Kano.
SHEKARA: 2018
SHAFUKA: 175
MAI SHARHI: Ibrahim Sheme

TUN a cikin shekarar 2018 ka buga wannan littafin mai suna “Salatin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam: Matsayinsa Da Fa’idojinsa Da Sigoginsa”, amma waɗansu dalilai su ka sa bai fito ba sai a bana.

Marubuciyar littafin, Hajiya Hajara Muhammad Kabir, ta rubuta wasu littattafan a baya, amma wannan shi ne ta yi kacokam kan wani abu da ya shafi addini kai-tsaye. Ta ɗau tsawon shekaru shida ta na bincike a kan sa tare da rubuta shi. Za a iya cewa littafin ƙarami ne, amma fa abin da ya qunsa babba ne.
Kamar yadda sunan sa ya faɗa, littafin ya na magana ne kan muhimmancin salatin Annabi (SAW). Kowane Musulmi ya san matsayin Manzon Allah a addinin Musulunci, amma ba kowa ba ne ya ɗauki salatin Annabi da muhimmanci ko ma ya san menene salatin. Wannan littafin zai ilmantar da duk mai karatu a wannan ɓangaren.

Na karanta littafin a tsanake, na ga muhimmancin sa, don haka na ga ya dace in sanar da mutane abin da na tsinta a ciki don a nema a karanta. Domin a lokacin da ake ta fafutikar neman duniya, to neman lahira ma muhimmin aiki ne da ya kamata kowane Musulmi ya sadaukar da rayuwar sa gare shi.

An buɗe littafin da ayar Alƙur’ani ta 56 daga Surar Al-Ahzab inda Allah (SWT) ya ke cewa: “Haƙiƙa, Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku waɗanda ku ka yi imani, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintawa a gare shi.” (Tarjamar da Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ya yi a cikin 1979).

Manufar kawo wannan aya ita ce domin a nusar da mai karatu cewa yi wa Annabi (SAW) salati umurni ne kai-tsaye daga Allah zuwa ga muminai ne, wato waɗanda su ka yi imani da Allah da manzon sa. Kuma an ankarar da mu cewa shi kan sa Allah da mala’ikun sa su na yi wa Annabi salati; in kuwa haka ne, to wanene zai fi ƙarfin ya yi masa salati?

Don a fahimci lamarin cikin sauƙi, an karkasa wannan littafin zuwa gida huɗu, kowanne da abin da ya ƙunsa. A sashe na farko, an share fage ne da tarihin Manzo (SAW) a taƙaice, wato daga kafin samuwar sa a haife (tun ya na a matsayin haske), zuwa samuwar sa a matsayin mutum ta hanyar nasaba da haihuwa, da ayyukan da ya yi a matsayin ɗan kasuwa, magidanci, Annabi, kuma jagora a siyasance har dai zuwa wafatin sa.
Da yake yawancin Musulmi sun san tarihin Manzo (SAW), za a iya cewa wannan sashe tamkar shimfiɗa ne na bayanan da ke gaba, domin ba zai yiwu a yi bayani kan salatin Fiyayyen Halitta ba tare da an kawo tarihin sa ba. Don haka sashen (daga shafi na 2 zuwa na 34) ya ƙunshi abubuwa da dama daga sirar Manzo (SAW). Haƙiƙa, wannan sashe babbar tunatarwa ce ko ga wanda ya yi zurfi a sanin sira. Za ma a iya cewa akwai bayanan da ba kowane ɗalibin sira ba ne farat ɗaya zai faɗa maka wasu abubuwan daga yalwataccen tarihin Manzo, misali sunan garin da mahaifiyar Annabi ta rasu ko kuma a ƙofar gidan waye ya fara gina masallacin sa a Madina, da wanda ya fara koya wa Annabi yadda ake yin sallah da kuma wanda shi Manzo ya fara koya mawa.

Da yake an bada tarihin a taƙaice ne, bai ƙunshi dukkan al’amaran rayuwar Annabi da zurfi ba. Misali, a shafi na 17, marubuciyar ta ce, “Annabi (SAW) ya tura wa mutanen Madina wanda zai riƙa karantar da su al’amuran addinin” Musulunci, amma ba ta faɗi sunan wanda Manzo ya tura ɗin ba, wato Mus’ab bin Umayr.
Sashe na biyu na littafin ya na ƙunshe da bayani kan salatin Annabi (SAW) daga ma’anar kalmar “salati” da hukunce-hukuncen sa da lokutan da ake yin sa da yadda ake yin sa da ƙarfafawar yin sa. Marubuciyar ta ruwaito malaman hadisi da na fiƙihu da sauran fannonin ilimin Musulunci sun kawo ma’anonin kalmar. A taƙaice, salati na nufin “addu’a ko sanya albarka ko yin godiya ko kuma yabawa.” Akwai wasu ma’anonin da ta kawo waɗanda ba su nesanta sosai da wannan ɗin ba.

A nan, ya kamata a sani cewa yi wa Annabi (SAW) salati ba yi masa bauta ba ne. Wani aiki ne na inganta bautar Allah. Marubuciyar ta ruwaito Annabi ya na faɗi da kan sa, a sashen tarihin sa da ta kawo, cewa babu abin bauta wa sai Allah shi ɗaya tal. A cewar ta, “Salatin Annabi Muhammadu (SAW) wani nau’in ibada ne na zikirin Allah da addu’a da nufin girmamawa da yabawa da karramawa da nuna ƙauna da godiyar alheri ga fiyayyen halittun Allah, Annabi Muhammadu (SAW)”.

Har ila yau, a sashen ta kawo hukuncin yin salati ga Annabi, da falalar yin sa (misali samun ceto a ranar Ƙiyama da kuma samun Aljanna), da lokutan da su ka kamata a yawaita salatin (misali ranar Juma’a, lokacin shiga masallaci da lokacin karanta Tahiya a cikin sallah).

Marubuciyar ta kawo hadisai da su ka tabbatar da wajibcin salatin Annabi. A wata gaɓar, an wajabta shi saboda ayar Allah da aka ambata “ta yi umurni bisa wajibci” ne kamar yadda wasu malamai su ka yi ittifaƙi.

Kashi na uku ya na ɗauke da ire-ire da lafuzzan salatin Annabi (SAW). Wannan ya ƙunshi yanaye-yanayen salatin daga hadisai (kai-tsaye daga Manzo, misali salatin Ibrahimiyya) da shaihunnai. An kawo ire-iren su guda 16 a sashen.
A kashi na ƙarshe, an kawo jerin wasu daga cikin littattafan salatin Annabi (SAW). Sun haxa da salatin Hassan da Hussaini da na Basha’iril-Khairati na Sidi Abdulƙadir Jelani da salatil-Muqaddam na Alfu-Alfi.

A ƙarshen littafin, Malama Hajara ta kawo jawabin kammalawa inda ta faɗi burin ta na rubuta shi, kuma ta jero littattafan da ta duba wajen wannan bincike, waɗanda mai karatu zai iya duba su domin samun ƙarin bayani. Sannan akwai ratayen bayanai har uku: ɗaya a kan kyawawan sunaye daban-daban da ake yi wa Manzo (SAW) laƙabi da su, ɗaya a kan wasu daga cikin hanyoyin begen Annabi (SAW), sai kuma ɗayan inda aka fassara wasu taƙaitattun kalmomi, misali ma’anar “radhiyallahu anhu” ko “rahimahullah”. Dukkan waɗannan ratayoyi muhimmai ne wajen samun cikar imani da Annabi da saƙon da ya zo wa duniya da shi.

Abubuwan burgewa game da wannan littafi sun haɗa da yadda aka rubuta shi cikin sassauƙar Hausa yadda kowa zai gane; an kawo misalan kowane abu da ake magana a kan sa, kuma an kawo misalan ne a cikin rubutu kala uku: rubutun Larabci da juyawa cikin rubutun Romanci da kuma fassarawa da Hausa. Haka kuma ɗab’in ya yi kyau matuƙa.

A ƙarshe, ina so a fahimci muhimmancin littafin wajen yadda mutane da dama ke neman hanyar da za su bi domin kyautata kusancin su da Allah (SWT) ta hanyar yi wa Manzo (SAW) masa salati, amma ba su sani ba ko kuma sanin nasu bai yi zurfi ba. Yawanci waɗannan hanyoyi sai an je gun manyan malamai sannan a samu. Su kuma malaman, galibi su kan bayar da su ne a dunƙule, waxanda su ke zavowa daga cikin wagagen littattafan da ke cikin taskar su. Haka kuma salatin da su ke bayarwa cikin Larabci ne, wanda sai mutum ya zauna a gaban su ya yi tilawar abin da su ke karantar da shi. Wannan littafi zai sauƙaƙa hawa kan wannan hanya, domin kuwa ga littafin a hannun mutum, kuma da Hausa.

A nan, ba ana nufin da Hausar ce mutum zai yi salati ba, amma fassara jerin salatai da malamar ta yi zuwa Hausa zai sanar da mutum abin da ya ke kawowa cikin Larabcin.

Kamar yadda editan littafin, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero, Kano, ya faɗa a ta’aliƙin da ya yi: “Wannan littafi na salati babban jari ne mai kai mutum Musulmi zuwa ga sa’adar rayuwa ta duniya da ta lahira, musamman idan aka lazimci karanta shi da yin sa da kuma tsarewa a kan aiwatar da shi tare da kyautata niyya a kan haka.”

Allah ya saka wa Malama Hajara da mafifin alheri kan wannan muhimmin aiki da ta yi, ya sa ya zame mata hanyar samun biyan buƙatar ganin Fiyayyen Halitta a gobe ƙiyama, amin.

Za a ƙaddamar da wannan littafi a ranar Asabar, 20 ga Fabrairu, 2021 a fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a birnin Kano.