Lookman ya cancanci kyautar gwarzon CAF na bana – Kanu

Tsohon ɗan wasan Super Eagles Nwankwo Kanu na neman Ademola Lookman ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan CAF na shekarar 2024.

Lookman ya taka rawar gani sosai a wannan shekarar.

Dan wasan mai shekaru 27 shi ne kaɗai ɗan Afirka da aka zaɓa a matsayin ɗan takarar kyautar Ballon d’or na 2024.

Kanu, wanda ya lashe kyautar sau biyu a baya, ya yi amannar cewa tauraron Atalanta ne kawai wanda ya dace ya lashe kyautar a wannan karon.

“Lookman ƙwararren ɗan wasa ne, mai haƙuri, yana aiki tuƙuru kuma yana da biyayya, na yi imanin zai yi nasara,” Kanu ya shaida wa Brila FM.

“Ban san wani ɗan wasan Afrika da ya yi ƙoƙari fiye da shi a bana ba.