Luca Modric ya buga wa Real Madrid wasa na 550 ranar Talata a karawar da AC Milan ta yi nasara 3-1 a Champions League da suka yi a Santiago Bernabeu.
Dan ƙasar Crotia, ya fara yi wa Real tamaula ranar 29 ga watan Agustan 2012 a Super Cup da Barcelona, shi ne na shida a yawan buga wa ƙungiyar tamaula a tarihi.
Kyaftin ɗin ƙungiyar yana kaka ta 13 a Real Madrid a bana, wanda shi ne kan gaba a yawan lashe kofuna a ƙungiyar mai 27 jimilla.
Ya lashe European Cups shida da Club World Cups biyar da European Super Cups biyar da La Liga huɗu da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups biyar.
Ga jerin wasa 550 da ya buga wa Real Madrid a dukan fafatawa:
Ya buga wasa 370 a La Liga da 124 a Champions League da 29 a Copa del Rey da 13 a Spanish Super Cup da takwas a Club World Cup da kuma shida a European Super Cup.
Kakar da ya buga wa Real wasa da yawa ita ce 2012/13 da ya yi karawa 53 da kuma ta 2022/23 da ya buga wasa 52.
Kawo yanzu ya ci wa Real Madrid ƙwallo 39.