Magidanci ya yanke mazaƙutarsa a Borno

Spread the love



An ceto wani mutum mai shekara 50 ya yi yunƙurin kashe kansa ta hanyar gigarawa mazaƙutarsa wuƙa a garin Bama na Jihar Borno.

Lamarin wanda ya afku a yammacin ranar Juma’a a unguwar Hausari, al’ummar yankin ne suka kai masa ɗauki.

Shaidu sun ce mutumin ya daɓa wa kansa wuƙa har sau uku a ciki, kafin ya yanke mazaƙutarsa da wuƙar.

An ce ya aikata hakan ne saboda tsohuwar matarsa, daga garin Konduga, wadda ya yi wa saki uku, ta ƙi komawa gidansa.

’Yan sanda sun jagoranci tawagar ’yan sintiri zuwa wurin, inda suka gano tare da ƙwace wuƙar, sannan suka kwashi magidancin zuwa Babban Asibitin Bama, inda yake karɓar magani.
Majiyoyi sun ce an miƙa lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) da ke Maiduguri, domin ci gaba da bincike.

By ukarofi