Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Jinƙai da Agaji, Nentawe Yilwatda ya ce, Gwamnatin Tarayya na shirin bai wa gidaje 15 da kuma ɗaiɗaikun mutane miliyan 75 tallafin kuɗaɗe. A cewarsa, za a biya kowane magidanci Naira 25,000 duk wata sau uku a shekara.
Mista Yilwatda ya ce, matakin wani ɓangare ne na yunƙurin da shugaba Bola Tinubu ke yi na ganin an shawo kan matsalolin da ke tattare da tattalin arziki ga marasa ƙarfi a Nijeriya.
“Shugaban wasa ya baiwa shirin fifiko, akwai tsare-tsare da ya kawo don ganin ko hakan zai iya sauƙaƙa wa mutane ƙalubalen rayuwa,” inji shi a ranar Litinin ɗin da ta gabata a gidan Talabijin na Channels.
“Na ɗaya, ya ce ya kamata mu tuntuɓi mutane miliyan 15 da suka ci gajiyar tallafin a ƙarƙashin shirin kuɗi domin su taimaka wajen rage raɗaɗin ’yan Nijeriya da suke a matakin ƙasa a ƙarƙashin rajistar zamantakewarmu. Waɗannan gidaje ne, ba ɗaiɗaikun mutane ba. Kowane gida, muna tsammanin yana da kusan mutane biyar.
“Don haka, idan muka kasance muna kaiwa gidaje miliyan 15 shirin, hakan na nufin shugaban ƙasa yana tsammanin shirin ya kai ga ‘yan Nijeriya miliyan 75 da wannan tallafin kuɗaɗe.”
Ministan ya ce, gwamnatin tarayya ta iya kaiwa ga mutane miliyan biyar kawo yanzu kuma tana aikin tsaftace rajistar zamantakewa.
