Zargin cin zarafi: Kwastom ta dakatar da sintirin bakin iyakokin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta sanar da dakatar da aikin sintirin haɗin gwiwar jami’an tsaro na bakin iyakokin ƙasar ‘Joint Border Patrol Team’ (JBPT).

Kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

A ranar 11 ga Disamba ne majalisar wakilai ta ba kwamitinta na kwastam umarnin gudanar da bincike kan ayyukan jami’an kwastom a bakin iyakokin ƙasar bayan zarge-zargen almundahana da cin zarafin ’yan ƙasar.

Amma kakakin rundunar ya ce hukumar ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na inganta tsaron bakin iyakokin domin fuskantar 2025.

Maiwada ya ƙara da cewa, dakatar da jami’an ba zai zama barazana ga tsaron bakin iyakokin ƙasar ba, inda ya ƙara da cewa za su ɗauki matakin zamanantar da ayyukan hukumar domin tabbatar da tsaron ƙasar.

Asali an kafa dakarun haɗin gwiwar ne a ƙarƙashin kulawar ofishin NSA domin yaƙi da fasa-ƙauri da kwarorowar baƙin haure da wasu manyan laifuka.

By ukarofi