Mahaifin Gwamnan Anambra ya rasu yana da shekara 92

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya rasa mahaifinsa, Pa Simon Soludo.

Pa Soludo ya rasu ne a ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya, inda ya bar duniya yana da shekara 92.

Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Mr Christian Aburime ne ya sanar da rasuwar marigayin cikin wata gajeriyar sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce, Pa Soludo ya rasu ya bar ‘ya’ya takwas da jikoki 22 da tattaɓa kunne shida.