Yadda za ki gyara nononki ta hanyar amfani da tumfafiya

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, Allah Ya ƙara mana lafiya da zaman lafiya.

Da yardar mai kowa da komai, shafin Kwalliya na jaridar Manhaja na wannan makon zai waiwayi mata da ke neman hanyar gyara nonuwansu, kamar yadda muka sani a gyaran jiki, nono zai shiga a layin farko ga mata, kasancewar sa babban alama da ka iya bambanta mace da namiji, kuma kamar yadda matar manzoni rahma, Nana Aisha Allah Ya ƙara yarda da ita ta ce, gemu ne adon maza, yayin da nonuwa suke kwalliyar mata.

Kenan gyara nono zai iya zama babbar kwalliya da ya kamata mata su sa a gaba fiye da kowacce irin kwalliya.

A wannan darasi za mu kowa wa mata hanyar gyara nono ta amfani da abu ɗaya, wato tumfafiya. Kuma haɗi ne dai bai tsaya a iya matan aure da suke shayarwa ko suka hayayyafa nonon ya zube ba, har ‘yan mata da suke fatan nononsu ya tsaya a yadda yake ba tare da ya zube ba.

A wani vangare, wannan haɗi da muke shirin zayyanowa masu karatu magani ne ga wasu matsalolin nono, kamar; ciwon nono(amma ba da ciwon da wasu daga manyan cutuka ke haifarwa ba, kamar ciwon daji da sauransu), sanyin nono da makarantan su.

Ta yaya za a haɗa wannan haɗi?

Za ki nemo ƙwallon tumfafiya, ba tare da an fashe shi ba, za a shanya shi (kuma a guje wa yin abinda zai fashe kafin a shanya shi), sai ya bushe sosai, kafin a dake shi ya koma gari.

Za a iya tankaxewa, amma abinda ya fi, za a cire wani farin abu mai kama da kaɗa, wanda shi ba zai daku ba, sannan a nemo man shanu mai kyau, shi ma ɗanye wanda ba a soya ba.

Za a haɗa waɗannan ababe biyu a wuri guda, a cakuɗe su sosai, sai a samu mazubi mai marfi, a saka, a rufe.

Za ki dinga shafawa nonuwanki, amma zai kasance kina murzawa tsayin lokaci, ba iya shafawa ba. Ma’ana, idan ki ka shafa, za ki dinga sanya hannu kina matsawa, tamkar dai kina fatan ki shigar da maganin ga cikin fatar ba iya samanta ba.

Wannan haɗin zai iya qara wa mace mai shayarwa ruwan nono, ya kuma cika nonuwan da suka zube, sannan ya tsayar da waɗanda ba su zube ba, ga uwa uba maganin wasu daga cikin cututan nono kamar yadda muka faɗa.

Abin lura:

Sanin mu ne man shanu ɗanye na da ƙamshin da ba kowa ne yake sha’awar jinsa a jikinsa ko jikin matarshi ba, don haka yake da muhimmanci uwargida ta san lokuta da suka fi dacewa ta yi amfani da wannan daɗin, da kuma yadda za ta kula da jikinta bayan ta tabbatar haɗin ya gama shegewa a inda aka saka shi.

Ma’ana dai, ta tanadi turare musamman don tabbatar da idan ta yi wanka za ta iya vatar da warin man daga jikinta.