Tarihin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaini CON, RTA (2)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Cigaba daga makon da ya gabata.

Ya na iya zama abin farin ciki sanin cewa, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi shekaru ashirin ne kacal (1944-1964) a matsayin ɗalibi, kuma ya samu kusan dukkan horon da ya yi a Nijeriya. Duk da haka, wannan ba ya na nufin cewa dukkan malamansa ’yan Nijeriya ne ba. Amma duk da haka, ya kasance masani na gida, wadda aka samar a cikin gida ta hanyar tsarin Tsangaya.

Watau, horon da ya samu a cikin tsarin karatun gida ne ya ba shi damar kasancewa mashahuri a ƙasashen duniya, da kuma karrama shi a matsayin qwararren malami.

Waɗannan su ne mas’alolin da malamai suke magana a kai: nasikh wal mansukh ko asbabul nuzul. Ya na kuma iya bayar da dukkan waɗannan bayanai a kan kowace ayar Al-Ƙur’ani, sai dai in da raunin ɗan Adam ya gaza.

Bayan waɗannan fagage, Sheikh Ibrahim Saleh ya bayar da muhimmanci sosai ga karatun Tauhidi da Fiƙihu. Ya kuma karanta mafi yawan muhimman littattafan da ake da su a kan tauhidi. Sannan kuma ya fahimci tushe da yanayin bambance-bambance a tsakanin mazhabobi. Fiƙihu na Mazhabar Malikiyya shi ma wani sarari ne a wurinsa.

Sai dai kuma, Sheikh Sharif, ya ce ya fi sha’awar vangaren ilimin Al-Ƙur’ani da Hadisi kuma a nan ne ya fi ƙwarewa. Sannan ya haddace Hadisan da suke cikin Bukhari da Muslim da sauran manyan litattafan hadisai.

Hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mu’amalar da yake yi da masana da mabiya sauran mazhabobi.

Wasu daga cikin ayyukansa su ne; Kafa Kwalejin Kimiyya da Ilimin Addinin Musulunci (Annahda), a shekara ta 1957.

A shekarar 1963, Sheikh Ibrahim Saleh ya yi aiki wajen gudanar da ayyukan gwamnatin yankin Arewa, wadda ya nemi shigar da makarantun Tsangaya cikin tsarin ilimin zamani, a lardin Borno.

A lokacin da gwamnatin jihar Borno ta kafa kwalejin koyar da shari’a da addinin Musulunci ta Borno (BOCOLIS) an naɗa shi ne domin ya taimaka wajen tsara shirye-shiryenta na ilimi.

Kuma daga baya ya zama mamba na Hukumar Gudanarwa na Makarantar. Haka nan, daga 1984 zuwa 1990, ya zama Shugaban Hukumar. Amma a shekarar 1990 aka sake naɗa shi Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiha. Ya kuma kasance a sabon ofishin nasa na kusan shekaru biyu, sannan aka mayar da shi tsohon muqamin sa na (BOCOLIS) a matsayin Shugaban Hukumar Gudanarwa.

Sheikh Ibrahim Saleh, ya kuma ƙulla kyakkyawar alaqa da gwamnatoci daban-daban tun daga 1976, a matakin tarayya.

Ya kasance mamba na kwamitocin da ake kafawa don ba da shawara ko jagoranci gwamnati kan wasu manufofinta da ke da alaƙa da addini.

Ya kuma kasance ɗaya daga cikin waɗanda gwamnatin ƙasar ke yawan tura wa zuwa ƙasashe a matsayin wakilan gwamnati ko kuma cikin wata tawaga zuwa ƙasashe kamar; Saudi Arabiya, Iran, Masar, Turkiyya, Libiya, Morko, Malaysia, Indonesia, Pakistan, Senegal, Iraq, Sudan, da sauran su.

Haka kuma an gayyace shi da dama domin gudanar da Tafsiri a gidan gwamnati da ke Legas, a cikin watan Ramadan, daga shugabannin da suka gabata daban-daban.

Ya kasance a sahun gaba wajen shirye-shiryen ƙarfafa haɗin kan Musulmi da tattaunawa tsakanin addinai domin samun zaman lafiya a Nijeriya da ƙasashen waje.

A cikin wata hira (BBC Hausa) ya ce, ya kamata malamai su daina hauragiya da zage-zagen juna. “Kamata ya yi su haɗa kai wajen ilimantar da al’umma.”

Sannan ya kuma koka kan yadda ya ce ake siyasa a Nijeriya ba don cigaban al’umma ba.

Sheikh Ibrahim Saleh, ya na da ɗalibai da almajirai masu tarin yawa a faɗin ƙasashen musulmi da na larabawa, su na kuma neman shiriya ta addini da inganta karatun boko.

Haka nan, mabiyansa a kodayaushe su na tare da shi ta kowane fanni da ya shafi rayuwar su. An kuma rubuta wasu daga cikin ƙasidunsa da littattafansa kai-tsaye ga wasu batutuwa na shari’a da koyarwa.

A cikin babban fagagensa na sha’awar ilimi da bincike, ya rubuta litattafai da ƙasidu sama da ɗari huɗu (400), da kuma takardu a wajen gabatar da taro sama da ɗari (100), waɗanda duk a cikin harshen Larabci, sun haɗa da: Ilimomin Al-Kur’ani, Hadisai, Tarihi, Falsafa, Fiƙihun Musulunci, Ilimin Taurari, Adabin Larabci, Ilimin Harsuna, Kimiyyar Sufanci, Siyasar Musulunci, Dokokin Musulunci da Matsayar Gado, Zaman Lafiya Tsakanin Ƙasashe, Ainihin mutuntaka da ’yancin kai, da kuma sauran batutuwa daban-daban.

Baya ga xɗimbin ayyukan koyarwa da bincike, Sheikh Ibrahim Saleh ya kuma jagoranci ko shiga cikin ayyukan ƙungiyoyin Musulunci na ƙasa da na ƙasa da aasa tsawon shekaru, wadda sun haɗa da;

  • Shugaban Kwamitin Fatawa na Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci (SCIA) da Jama’at Nasril Islam (JNI).
  • Shugaban Majalisar Musulmi a Nijeriya (AMIN).
  • Shugaba kuma wadda ya kafa ƙungiyar Islamic Renaissance Organization International (IROI).

Mataimakin Babban Sakatare Janar na Jagorancin Jama’ar Musulmi na Duniya (GIWPL), har zuwa 2010.

  • Mamba a Majalisar Harkokin Addini ta Nijeriya (NIREC).
  • Mamba a Vision 2010.
  • Wadda ya kafa kuma Memba na Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya (IFMS), Makka.
  • Mamba a Majalisar Zartarwa ta Ƙungiyar Malaman Musulmi ta Duniya (IUMS), Ireland (tare da hedikwata a Doha har 2010).
  • Shugaban Kwamitin Ba da Shawarar Kuɗi na Ƙwararru (FRACE), na Babban Bankin Najeriya (CBN). Shi ne Shugaban Sashen Shari’a na Kasuwancin Musulunci, (CBN) tun 2012.
  • Ɗaya daga cikin waɗanda suka Majalisar Dattawan Musulmi (CME) Abu Dhabi United Arab Emirates.
  • Mamba A Cikin Kwamitin Amintattu na Hukumar Ba da Agaji ta Duniya.
  • Mamba na Kwamitin Amintattu na Ƙungiyar Yaɗa Addinin Musulunci (Sudan).
  • Wakilin Kwamitin Amintattu Musɗaf Afriƙiya (sudan).
  • Mamba Kwamitin Amintattu na Majalisar Karatun Al-Ƙur’ani, Jihar Borno.
  • Mamba Kwamitin Amintattu na Masallacin Ƙasa, Abuja.
  • Ɗaya daga cikin wadda suka damar da Ƙungiyar Malaman Musulunci a Afirka (Morocco).

Sakamakon haka, tare da jinjinawa da irin gudunmowar da ya bayar ga addinin Musulunci, da kuma ci gaba da ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabambantan ra’ayi, Sheikh Ibrahim Saleh ya samu lambobin yabo ta ƙasa da ƙasa. Waɗannan sun haɗa da:

  1. Takardar shaidar karramawa daga Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa reshen jihar Borno, 1985.
  2. Kyautar lambar yabo ta Masarawa ta farko a fannin fasaha da kimiyya (Wisam Al-Jamhuriya), wadda shugaban Masar, Muhammad Hosni Mubarak, Jamhuriyar Larabawa ta Masar, ya bayar, 1993.
  3. Shaidar karramawa daga hannun Ɗalibai na ɓangaren Lauyoyi, na Jami’ar Midogray, 1995.
  4. Shaidar daga Karramawa daga Ɗalibai na ɓangaren Shari’ar Addinin Musulunci, 1995.
  5. Takardun Shaidar Yabo daga Sashen Agajin Gaggawa na Jama’atul Nasirul Islam Group, 1996.
  6. Takardar shaidar karramawa da lambar yabo ta Da’awah ta Musulunci, wadda cibiyar Abi Alnnour Islamic Foundation da Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Syria, 1997 suka gabatar.
  7. Kyautar Daraja ta Farko ta Majagaba a cikin Hidimar Al’umma (Wisam Elriyada), wadda Jagoran juyin-juya halin Libiya Kanar Mu’ammar Gaddafi, Libya, 1998 ya bayar.
  8. Lambar Yabo ta (Dir’a-Daawah), wadda Ƙungiyar Kira Zuwa Ga Addinin Musulunci ta Duniya, Libya, 1998.
  9. Lambar Yabo ta “Al-Imam Abu Ala’za’m” (Imam Gold Medal), Alƙahira, 1998.
  10. Kyautar Daraja ta Farko a kan Rubutu (Afro-Asian Writer of the Year 2004), wadda Ƙungiyar Afro-Asiya ta Masar ta gabatar, Alƙahira, 2004.
  11. Kwamandan oda na Niger (CON), wadda shugaban ƙasa (Umaru Musa ’Yar’adua) kuma babban kwamandan rundunar sojojin tarayyar Nijeriya, Abuja, 2008, ya gabatar masa.
  12. Digiri na uku na Kimiyya (HNORIS COUSA) da aka ba shi, a wajen taron karo na Uku na Jami’ar Turkish Nile ta Nijeriya da ke Abuja, ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2015.

Bugu da ƙari, an sanyawa wane Masallaci sunansa a Jamhuriyar Nijar, (Sheikh Sharif Ibrahim Ibn Saleh Mosque, Niger).