Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan jan hankalin da Amurka ta yi wa ‘yan ƙasar mazauna Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta maida martani kan gargaɗin da ƙasar Amurka ta yi wa ‘ya’yanta mazauna Nijeriya game da zama a otel-otel na ƙasar, tana mai jaddada buƙatar da a daina biye wa batutuwan da ka iya haifar da rarraba kawuna.

Kazalika, Gwamnatin Nijeriya ta bada tabbacin cikakken tsaro ga rayukan ‘yan ƙasar da ma baƙi mazauna ƙasar.

Har wa yau, ta ce ta ɗauki ingantattun matakan tsaro da suka haɗa da tattara bayanan tsaro, haɗa ƙarfi da hukumomin ƙasashen duniya da sauransu domin tabbatar da tsaron rayukan baƙi.

Waɗannan bayanai sun fito ne daga bakin Ministan Larabai da Wayar da Kai, Alh. Mohammed Idris, yayin ganawarsu da manyan editoci ranar Litinin a Abuja.

Da yake bayani, Ministan ya taɓo irin nasarorin da Gwamnatin Tarayya ta samu a ɓangaren tsaro da suka haɗa tarwatsa ‘yan bindiga a Jihar Kaduna, daƙile yunƙurin harin ta’addanci a Jihar Kano, kuɓutar da wasu masu yi ƙasa hidima da aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina da sauransu.

Kazalika, ya ce Rundunar Sojojin Ruwan Nijeriya (NAF) ta samu nasarar fatattakar ‘yan bindiga da ɓarayin daji a maɓuyarsu a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Don haka ya ce, “Abin da muka gani shawarwari ne waɗanda babu buƙatarsu, kuma hakan ka iya yin tasiri kan tattalin arziki da kuma ƙaranta ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen jawo hankalin masu zuba jari a ƙasa.”

Ya ƙara da cewa, “Gwamnatin Nijeriya ta bada himma wajen kyautata tsaron rayuwar ‘yan ƙasa da walwalar baƙin da ke ƙasar.

“Jami’an tsaronmu suna aiki ba dare, ba rana domin tabbatar da tsaron rayukan al’umma baki ɗaya,” in ji Ministan.