Mai gadin kasuwa ya sace wayoyin maƙudan kuɗaɗe

Dubun wani mai gadi ta cika bayan ya saci wayoyin hannu da kuɗinsu ya kai Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar a kasuwar da ya ke aikin gadi.

An gurfanar mai gadin, mai shekaru 25 a gaban kotun Mai Shari’a O. A. Taiwo, na kotun da ke Ikeja Jihar Legas.

Ana tuhumar mai gadin da aikata laifuka huɗu, haɗin baki, sata, fashi, da shiga wuri ba da izini ba, amma ya musanta zarge-zargen.

Ɗan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Raphael Donny, ya faɗa wa kotun cewa mai gadin tare da abokansa sun balla shagon wata ’yar kasuwa mai suna Winner Erebor a Ikeja a ranar 23 ga watan Yuni.

Daga nan suka sace wayoyi masu tsada na fiye da Naira Miliyan 1 da dubu ɗari biyar.

Hakan, a cewarsa, laifi ne da ya sava sashe na 307, 287, 309, da kuma 411 na kundin manyan laifukan Jihar Legas na 2015.

Alƙalin ya bada belin mai gadin kan Naira dubu 100 da sharaɗin zai kawo wanda zai tsaya masa wanda kuma ya mallaki makamantansu.

Daga baya alƙalin ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Agusta mai kamawa.