Ba ɓoyayye ba ne cewa giwaye suna daga cikin dabbobin da suka fi saurin shaƙuwa da mutane a duniyar nan, tare da samun shaidu da yawa na waɗannan halittun da ke nuna farin ciki, baƙin ciki, fushi, tausayi, har ma da ƙauna.
Amma sai dai a Indiya wata giwa ta kashe wata mata mai shekara 70 sannan ta je ta tattake gawarta a yayin jana’izarta.
Giwar ta tsere bayan ta yi wa matar mai suna Maya Murmu aika-aikar a lokacin da ta ke tara ruwa a ƙauyen Raipal da ke Gabashin Indiya, inji ’yan sanda.
Matar ta rasu a asibiti sakamakon raunukan da giwar ta yi mata.
Haka kuma, a yayin jana’izar marigayiyar a yammacin ranar, sai giwar ta je ta tattake gawarta a daidai lokacin da danginta su ke jana’izar marigayiyar, kamar yadda jaridar Press Trust of India ta ruwaito.
Giwar na tafiya sai ’yan uwan matar suka ci gaba da jana’izar. Bayanai sun ce, bayan giwar ta aikata hakan sai ta tsere daga gidan namun daji na Dalma da ke garin Mayurbhanj mai nisan kilomita 200 a cewar rahotanni.
A watan Okotban bara ma an samu rahoton wata giwa ta tattake wani tsoho mai yawon buɗe-ido, inda ta kashe shi a gaban ɗansa a ƙasar Zimbabwe.
Giwar ta kashe tsohon mai suna Michael Walsh, mai shekara 71 da ya ke tare da ɗansa mai shekara 41, lokacin da su ke tafiya da safe a dajin yankin da aka killace namun daji na Mana Pools National Park.
Suna da nisan mil 40 da motarsu, lokacin da giwar ta kai wa Mista Walsh hari. Kakakin Gandun Dajin Mana Pools National Park, Tinashe Farawo ya ce, “dan marigayin yana gani giwar ta kashe mahaifinsa.”
Walsh, wanda likitan dabbobi ne daga Cape Town da ke Afirka ta Kudu, wanda ya je yawon buɗe-idon da ya saba a Mana Pool.
Ya rasu ne bayan shekara 35 da kwanaki bayan wata giwa ta tattake wani shugaban mafarauta a yankin bictoria Falls da ke Yammacin Zimbabwe.
Hukumomin Kula da Yawon Shakatawa a Zimbabwe da ƙungiyoyin kare muhalli suna ci gaba da ba da rahotannin qaruwar rikici a tsakanin mutane da namun daji a ’yan shekarun nan.
Bisa ƙididdigar Gidauniyar Kula da Namun Daji ta Duniya, giwaye suna kashe mutane 100 zuwa 300 a kowace shekara a Indiya (WWF).
Kalaman wasu game da abin giwar ta yi Wasu masu amfani da shafin Tuwita sun yi tsokaci tare da tambaya game da ainihin abin da matar ta yi wa giwar har ta bi ta wajen jana’izarta ta tattake gawarta.
Amsar da wasu masu martani ke bayyanawa a shafukan Tuwita da Tik Tok ita ce, kila matar ta yi yunqurin farautar ’yar giwar ce ko yunƙurin kashe jaririyar giwar tare da korar uwar.
A cewar wasu masu amfani da shafukan Intanet, ba a samu shaidar cewa giwar ta kashe matar ce saboda tana yunƙurin kashe mata ’ya ba.
Wasu rahotanni sun ce, Murmu ta je ɗibar ruwa ne a ƙauyen Raipai da ke kusa da Gidan Adana Namun Daji na Dalma na Wildlife Sanctuary, sai aka ji kukan matar.
Da aka je sai aka samu ta raunana ta kamar yadda jaridar The Times of India ta ruwaito. Matar ta yi yunƙurin guje wa giwar, amma hakan ya ci tura.
Mutanen ƙauyen sun yi yunƙurin ceto ta, daga bisani aka sanar da rasuwarta a asibiti.
A ranar da ta rasu mutanen ƙauyen sun yi shirin jana’izarta, sai giwar da ’yan uwanta giwaye 11 suka fito daga dajin, inda suka lalata gidaje uku a ƙauyen, sannan suka tattake gawar Murmu.
“Aqalla mutum 1,144 ne dabbobin dawa suka kashe a tsakanin watan Afrilu 2014 zuwa Mayun, 2017. Mutune 1,052 daga cikinsu giwaye ne suka kashe su,” inji jaridar Guardian ta Ingila.