An gano Naira miliyan 540 a asusun malamar firamare

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Abuja, ta bai wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), umarnin karɓe Naira miliyan 120 daga hannun wata malamar makarantar firamare, Roseline Egbuha, da abokan aikinta da aka samu a asusun ajiyarta na banki.

Kuɗaɗen da aka ƙwace, da kuma motoci sun kai Naira miliyan 540 da aka gano a wajen matar, wadda malama ce a makarantar firamare ta Ozala da ke Abagana a Jihar Anambra.

Malamar da ke karɓar albashin N76,000 duk wata a lokacin da ICPC ta kama ta a 2020, ta ɓoye Naira miliyan 540 a asusun ajiyarta na bankin Guaranty Trust.

Wani bincike da ICPC ta gudanar ya nuna cewa, tana da hannu a almundahanar kuɗaɗe wanda hakan ya sa hukumar ta sanya wa asusun nata takunkumin hana cire kuɗi.

Sai dai kuma, an cire takunkumin da aka sanya wa asusun na Egbuha da abokan hularta bayan wani umarnin da wata Babbar Kotu da ke Abuja ta bayar, inda nan ta ke kuɗaɗen aka raba su sannan aka tura wasu asusun banki mallakar wasu masu gudanar da harkar canjin kuɗi.

Lauyan ICPC, Adesina Raheem, a cikin buƙatar da ya shigar a 2021 a gaban Mai Shari’a D. U. Okorowo, ya yi zargin cewa an yi amfani da haramtattun kuɗin wajen gudanar da ayyukan da ba su dace ba, bayan an raba su zuwa gida shida sannan aka tura wa mutane daban-daban.

Sauran abubuwan da aka kwace sun haɗa da motoci ƙirar Toyota Lexus da Venza.