Majalisar Dattawa ta fara sauraren ra’ayoyi kan ƙudirin gyaran dokar haraji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Dattawa ta fara gudanar da zama na kwanaki biyu don jin ra’ayoyi game da ƙudirin dokar gyaran haraji, inda ta haɗa masu-ruwa-da-tsaki daga ɓangaren harkokin tattali da kuɗi.

Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da Ministan Kuɗi da Tattali, Wale Edun; Shugaban Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji (FIRS), Zacch Adedeji; Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari; Mambobin Majalisar Zartarwa da jagororin wasu hukumomi da sauransu.

Shugaban kwamitin majalisar akan kuɗaɗe, Sanata Sani Musa ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaman cikin tsari kuma bisa gaskiya da adalci tare da la’akari da maslahar al’umma.

Ya ce, ana yin sauraron ra’ayoyin ne da manufar daidaita ƙudirorin dokar gyaran da yanayin harkokin tattali a Nijeriya.

Sanatan ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki da ɗaukacin al’umma da su shiga a dama da su a yayin tattaunawar don samar da tsarin da zai taimaka wa haɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

By Babaji