An yi garkuwa da tsohuwa a asibitin mahaukata na Dawanau a Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun yi garkuwa da wata tsohuwa mai shekaru 60 a Asibitin Mahaukata na Dawanau dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano.

Lamarin ya auku ne a lokacin da matar mai suna Talatu Ali ke wajen jiran likita domin duba lafiyar ƙwaƙwalwarta.

Wani ƙwararren mai sharhi akan daƙile ayyukan ta’addanci, mai suna Zagazola Makama ya ce ɗanta mai suna Nasiru Aliyu da wani Aliyu Garba wanda ƙani ne a wajenta, suka kai ta asibitin a ranar 19 ga watan Fabrairu.

A lokacin da suke jiran ganin likita ne lamarin ya auku inda suka duba ba su gan ta ba.

A ranar 21 ga wata ne aka kira Aliyu ta wata lamba, inda aka bayyana masa cewa garkuwa da ita aka yi, kuma tana tsare a hannunsu.

Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ba a cika samun irinsa ba a jihar duk da kasancewar ta ɗaya daga cikin jihohin Arewa ta Yamma da ke fama da matsalolin garkuwa da mutane da wasu nau’ukan ta’addanci.

By Babaji