
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Limaman Juma’a ta Ƙasa, ƙarƙarshin jagorancin Shaikh Muhammad Nasiru Adam, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Jihar Kano bisa shirinta na tantance ƙungiyoyn da ba na gwamnati ba.
Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a yayin ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce hakan abu ne mai muhimmanci ga al’umma da ma jihar baki ɗaya.
Ya ce, ayyukan wasu ƙungiyoyi sun ci karo da al’adu da addinan mutanen Kano waɗanda su kan yin munanan tasiri a gare su, don haka ya ke da muhimmanci a tantance su.
Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bai wa kwamitin tantancewar goyon baya ta hanyar ba su bayanan da suka buƙata don gudanar da ayyukansu cikin inganci.
Shaikh Muhammad Nasiru ya ƙara da cewa Musulunci ya tsara yadda harkokin kowacce ƙungiya za ta gudana, ya na mai bada misali da ayoyin Alkur’ani.
