Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministocin Buhari

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar dattawa a ranar Laraba ta tabbatar da naɗin ministoci bakwai da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa mata a makon jiya.

Waɗanda aka tantance sun haɗa da Ikoh Henry Ikechukwu daga jihar Abia da Umana Okon Umana daga jihar Akwa Ibom da Ekumankana Joseph Nkama daga jihar Ebonyi da kuma Nana Opiah daga jihar Imo .

Sauran sun haɗa da Umar Ibrahim El – Yakub daga jihar Kano, Adenola Adewole Adegoroye daga jihar Ondo da Udum Udi daga jihar Ribas.

Tabbatar da waɗanda aka naɗa ya biyo bayan tsauraran matakan tantancewa na tsawon sa’o’i huɗu a kan kowanne daga cikin waɗanda aka naɗa.

Amma waɗanda aka naɗa daga Jihohin Imo da Kano, sun yi rantsuwa, saboda a baya sun kasance mambobin majalisar wakilai a lokuta daban-daban tsakanin 2003 zuwa 2019.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan bayan tabbatar da hakan, ya buƙaci Ministocin, waɗanda aka zaɓa, da su bayar da iyawarsu a duk ofisoshin da aka ba su.

Ya ce, ƙarancin lokacin da za su yi hidima, bai kamata ya hana su yin tasirin da ake buƙata a cikin abin da aka ba su ba.