APC ta ci amanar ‘yan Nijeriya

Daga SANI MUSA DAITU

Tun bayan hawa karagar mulki na Jam’iyyar APC a 2015 Jam’iyyar ta kasa sauke nauyin data ɗora wa kanta na farfaɗo da al’ummarmu. Me ya sa hakan ta faru? Saboda bas u da manufa, ba su da tsari. Mulkin kawai suke so ko ta wanne hali. Al’ummarmu ta Giwa da Birnin Gwari ba mu amfana da komai daga mulki APC ba, face takaici da baƙinciki. Nauyi na farko dake kan Gwamnati shi ne, samar da tsaro da walwalar al’umma. Amma tun zuwan APC kan mulki, hakan ta gagara. Inda ta rusa mana zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta rusa mana ilimi inda dubban yara ba sa zuwa makaranta a yankinmu, sakamakon gazawar APC. Makarantunmu an rufe su, wasu sun lalace an kasa gyarawa.

A harkar kiwon lafiya, al’ummarmu sun daɗe da cire tsammani da dogaro a kan asibitin gwamnati a yankinmu, sakamakon an yi watsi da asibitin Gwamnati a harkar kiwon lafiya a acikin al’ummar mu. Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa a wannan shekarar tace, sama da kadada dubu talatin (hekter 30,000) ba za a noma ba a yankin ƙaramar hukumar Giwa. Baya ga lalata mana dukiya da ƙaruwar ayyukan kisa da garkuwa da mutane. Baya ga haka, wannan daminar ‘yan bindiga sun sa wa manoma haraji a wasu yankuna da Al’ummar za su yi noma. Ina za mu saka kanmu? Ga ‘yan gudun hijira da mata da yara ƙanana waɗanda ba su san makomarsu ba.

Wani abin baƙincikin shi ne, a cikin kwanakin nan majalisar dokokin jihar Kaduna ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Giwa a kan zargin tu’ammali da kuɗaɗen haram Naira Miliyan ɗari bakwai (N700,000,000), amma har yanzu ba mu ji wani mataki da hukumomi cin hanci da rashawa suka ɗauka ba.

A Birnin Gwari a zaɓen qannan hukumomin da ya gabata, mun ci zaɓe, aka murɗe mana. Yin hakan karan tsaye ne da tsarin demokaraɗiyya, inda har yanzu APC ta ƙi bin umurnin kotu gurin rantsar da zaɓaɓɓen shugaba wadda doka ta amince da shi don samar wa al’umma mafita.

A cikin gidan Jam’iyyar PDP akwai ‘yan kamashon tsaye waɗanda suke cin amanar jam’iyyar don son zuciyarsu. Waɗannan ba su da manufa, sai burinsu na son kai. To muna kira dukkan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da mu zo mu yi aiki tare, mu tashi mu jajirce mu ceto tattalin arziki da zaman lafiya a Nijeriyarmu ta hanyar zaɓen jam’iyyar PDP. Ya Allah ka ba mu zaman lafiya a Nijeriya Amin.

Sani Musa Daitu ya rubuto ne daga Kaduna
Imel: [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *