Ni ce mace ta farko da ta zama Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa – Zainab Talatu Ahmed

“Mace uwa ce komai ƙanƙantarta”

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Hajiya Zainab Talatu Ahmed tsohuwar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa (ssg) ce, mace ce ta farko data riƙe wannan muƙami a tarihin Jihar Nasarawa. A yanzu ita ce shugabar matan jam’iyyar APC a shiyar Nasarawa ta Yamma. A tattaunawar ta da wakilinmu, John D. Wada, ta bayyana tarihin rayuwanta da wasu shawarwari da zasu taimaki ‘yan uwanta mata. Ga dai yadda hirar ta kasance: 

MANHAJA: Mu fara da jin tarihinki a taƙaice.
HAJIYA TALATU: Sunana Hajiya Talatu Zainab Abdulmumin. An haife ni a garin Nasarawa dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa anan Jihar Nasarawa, a ranar 11 ga watan Afrilu a shekarar 1962. Na fara makarantan firamare ɗina a ‘Central primary School’ dake cikin garin Nasarawa. Daga nan sai na kammla a ‘Township primary School’ a Jos Jihar Filato. Sakandare ɗina kuma na yi ne a wani makarantan mata dake garin Jos da ake kira ‘Saint Peace College’ Jos. Daganan sai na wuce jami’ar Jos inda na yi karatun digiri ɗina na ɗaya. Na sake koma wannan jami’ar Jos daga bisani inda na yi karatun digiri ɗina na biyu. Bayan na kammala bautan ƙasa daga shekarar 1986 zuwa 1987 a makarantan koyar da ungwan zoma (school of nurse) dake garin Sakkwato, sai na samu aiki a jami’ar tarayya dake garin Nasarawa, watau bayan na koma gida kenan. Ina wurin tun daga shekarar 1987 har zuwa shekarar 2005 lokacin da maigirma tsohon gwamnan Jihar Nasarawa na farko wanda shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ne a yanzu watau Alhaji Abdullahi Adamu ya naɗa ni a matsayin babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi inda daga bisani aka koma dani ma’aikatar wasanni da yawon shaƙatawa. 

Daga nan sai zuwan mai cikakken iko wanda ya gaje shi watau gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Tanko Almakura ya koma dani ma’aikatar ilimi har yanzu a matsayin babbar sakatariya. Matsayin da nake riwe da shi kenan kafin Allah cikin ra’amansa ya kuma bani muƙamin sakatariyar gwamnatin Jihar Nasarawa (SSG). kuma kamar yadda ka sani a tarihi ni ce na fara riqe muƙamin a ɓangaren mata kenan. A taƙaice dai na yi shekaru 8 ina matsayin babbar sakatariya a ma’aikatun gwamnatin Jihar Nasarawa kamin na samu wannan muƙamin shugabar matan jam’iyyar mu ta APC a shiyar Nasarawa ta Yamma a yanzu. Wannan shi ne taƙaitattacen tarihin rayuwata kamar yadda ka tambaya.  

Hajiya Zainab

To, idan mun koma ɓangaren rayuwa a lokacin tasowa, wanne irin buri kike da shi a lokacin da kike ƙarama?
Ni dai tun tasowa na ba abin da nafi so kamar malantaka, watau koyarwa. Domin bazan iya sani ko don sha’awan yadda malamai ke koyarwa ne ko kuma don ni kaina mahaifina malamin makaranta ne. Kaga mahaifina yana ɗaya daga cikin tsofaffi da suka fara yin makarantan boko a wuraran mu har yakai ga bayan ya kammala karatunsa na boko, yazo yana koyarwa mutane. Saboda haka na fito ne daga gidan malamin makaranta. To wannan sha’awan ne yasa da na tafi karatu a jami’a na zaɓi fannin koyarwa. 

Na karanta harshen Turanci (English course). Dukka diri ɗina na farko da na biyu duk a fannin koyarwa ne. Amma daga bisani na ɗan kauce kaɗan daga wannan fanni inda na yi karatu na musamman a wani fanni a PHD ɗina. Amma nikan abin da nafi sha’awa watau burina da nake tasowa shi ne, kamar yadda na bayyana maka in zama malamar makaranta. Kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya taimaka shi daɗin ne na yi harma yau zan iya buga ƙirji in ce ni cikakkiyar malamar makaranta ce, don an yi min rajista da hukumar yi wa malaman Najeriya rajista (Teachers registration Council of Nigeria) Saboda haka ni ba malamar makaranta ce kawai a suna ba, ina da rajista da wannan hukuma dana bayyana maka.

Za mu so jin waɗanne irin halaye ne kika koya daga iyayenki baya ga sha’awar zama malama kamar mahaifinki?
A gaskiya abin dana koya gun iyaye na musamman shine haƙuri da juriya. A duk yanayi da ka tsinci kanka ka yi tawakkali da Allah cewa shi ne yake bayarwa ga wadda yaso kuma inda yaso. Saboda haka mun tashi ne cikin ƙoshin zucci. Kamai da ka samu sai ka ce alhamdu llilahi. Shi ya sa cikin rahamarSa, yau ba wadda zai gaya maka cewa ga shi nan dai anje an bi min ƙafa ko a fannin karatu ne ko a wasu fannoni daban. Tun da muka fara karatu har ga neman aiki da sauran su ba wanda zai gaya maka yau cewa mahaifinmu ya tashi yaje ya nemo wa kowannenmu, bai yi haka ba, don ya tabbata hazaƙanka da ƙwazonka ne za su baka abin da ya dace da rayuwanka. Shi dai ya ƙarfafa mu ne ya kuma ba mu goyon baya. Shi yasa dukkanmu a gidanmu kowa ya yi karatun boko don mu ‘ya’yan babanmu mun fi goma. Kuma a cikin rahamar Ubangiji dukkanmu muna da digiri. Wasu ma suna da mastas digiri wasu fiye da haka, kuma dukkanmu muna aiki. Kuma a cikin ayukan da muke yi mahaifinmu bai tava ai ko sule ɗaya a matsayin cin-hanci don a ɗaukaka matsayin ‘ya’yansa ko wani abu makamaicin haka ba. Yakan bar mu ne muyi amfani da ƙwaƙwalwanmu da Allah Ya ba mu wajen neman na kanmu. 

Kaga kamar abin da ke faruwa yau, za ka ga za an bi ta bayan fage a samo wa yaro aiki ko wani abu makamaicin haka. To an samo maka ba ka dace da muƙamin ba, ai za a iya gani. Saboda haka mahimmin abu da na koya wurin iyayena kamar yadda na bayyana maka shine, haƙuri da juriya da kuma rashin kwaɗayi. Domin mahaifinmu ya yi ta mana huɗuba cewa, idan har kayi haƙuri da abin da Allah Ya baka, to rayuwanka ba shakka zai zama ingantacce. Za ka ga mu’ammalar ka da jama’a babu wata matsala don ba ka sa kwaɗayi ciki ba. 

Shi ya sa a duk inda muke kuma duk ayyuka da muke yi, mahaifinmu yakan gaya mana cewa kada ka sa ido akan kuɗin jama’a, ka yi taka-tsantsan, ka ji tsoron Allah. Amanar da aka baka ka riƙe da gaskiya. Kuma shi mahaifina da nake maka bayyani akansa, nan watau Alhaji Ahmadu Tanko shiya fara buɗe ma’aikatar ma’aikatan Jihar Nasarawa (civel service commission).

Ya kuma bada tsarin yadda za a gudanar da harkokin ma’aikatan wannan jiha a fanni horo (discipline) dadai sauransu. Haka ne ma yasa yau idan ka ji ana bada tarihin ma’aikatan wannan jiha, za ka ji ana ai lokacin baba haka ake kirashi, anyi kaza an yi kaza. To kaga ba shakka ya kawo cigaba sosai a wajen horon ma’aikatan Jihar Nasarawa bakiɗaya, ba mu yaransa kawai ba. Ka ji wasu daga cikin halayen da iyayena suka koya min kenan.   

Waɗanne nasarori ki ka cimma a rayuwa?
To, ni dai bamai iya bayyana nasarori da na cimma a rayuwa na ba ne, don ina sadaukar da rayuwana ne wajen yi wa jama’a aiki. Saboda haka waɗanda nake yin aiki domin su ne zan so ace sun bayyana nasarori da na cimma a halin yanzu. 

Su ya kamata su san ko na taka muhimmiyar rawa a rayuwansu ko ban yi ba. Babban abin da ni dai nake gani na samu nasara akansa sosai shi ne, cikakken goyon baya da nake bawa gwamna Almakura don ba shi damar aiwatar da abin da aka zaɓe shi ya yi. Ina ba shi goyon baya ne don tabbatar cewa, abin da ya dace wa jama’a anyi shi. Kuma na samu nasarar yin haka ba wai yabon kai ba. Sauran nasarori kuma kamar yadda na bayyana ma ka jama’a da nake yin aiki domin su ne ya kamata su bayyana. Musamman ka ga wannan ofishina, ofishi ne dake aiwatar da abubuwa da gwamnati ta ce a yi. Ni kuma ina tabbatar an yi ɗin. Saboda haka ko na ci nasara ko banci ba jama’a ne ya kamata su zama alƙalai.

Da me ki ke so a dinga tunawa da ke da shi? 
To, ni dai kamar yadda na bayyana ma ka a baya ina sadaukar da lokaci na da komai da nake da shi ne wajen yi wa jama’a aiki. Saboda haka abin da zan so a ce an tuna dani idan bana nan shine, mace wadda ta taimaka wa jama’a sosai don cimma burinsu a rayuwa. Ta kuma kawo cigaba mai ɗaurewa a Jihar Nasarawa dama kasa bakiɗaya. Yawwa to, abin da nake so a tuna dani kenan.

Waɗanne wurare ne kike sha’awar zuwa a lokacin da ki ke hutu? 
To, ni dai kamar ko wacce ‘ya mace Musulma, ba inda nake sha’awan zuwa a duniya a kowanne lokaci kamar Ƙasar Saudiyya. Kaga na farko za ka je ne ka ga abin sha’awa, na biyu kuma shine, ibada. Domin idan kana wajen tamkar kana gaban Allah Subhanahu wa Ta’ala ne. Duk wani abin duniya ka zazzage watau ka aje gefe guda ka fuskanci Ubangiji. Saboda haka ba inda nake son zuwa kamar Ƙasar Saudiya, infa a waje kenan. Idan kuma a gida ne nan Nijeriya, ba inda nake son hutu kamar tare da iyayena, don har yanzu suna da rai. Nakan je can garinmu Nasarawa, inyi hutu da su, suna ba ni shawarwari.

Domin kaga har yanzu ni ‘ya ce fa a gun iyayena. Kuma har yanzu tunda suna da rai, ina sha’awan kasancewa tare da su kullum, don tsinto wasu abubuwa da suka kamata da za su gyara min rayuwa. Waɗannan wurarai biyu watau Saudiyya a ƙasashen waje, sai kuma garin mu Nasarawa tare da iyayena anan gida Nijeriya su nake sha’awan zuwa lokacin hutu na.

A cikin halayyar mata bakiɗaya, waɗaaanne ne kika fi sha’awa daga cikinsu?
Watau halaye masu kyau su ne, sanin yakamata da riƙon amana da gaskiya. Kisan ke mace ce kuma ki san halayen da suka dace mace ta riƙa nunawa. Domin Allah subhanahu wa Ta’alla ya ba mu mata wasu umurnin da suka zamanto cikamaki ga halayen maza. Kaga bai dace ace mace ta riƙa ganin kanta kamar ita ce namiji ba. Domin kowa Allah ya ba shi nashi umurni. Saboda haka inaso inga mace mai natsuwa mai sanin ya kamata mai kuma ladabi da biyayya, wanda idan aka ce bari ta bari. 

Kada a samu mace ta zama fitinanniya a gun jama’a don irin wannan hali bai dace da ita ba. Ina so mace mai son zaman lafiya a duk yadda ta samu kanta, domin ita uwa ce komai ƙanƙantanta. Ya kamata ta zama uwa ta zama kanwa ta kuma zama ‘ya. 

Wannan ladabi daya kamata ace tana nuna su a kowanne lokaci. Ba a santa da tayar da zaune tsaye ba. Idan ana hayaniya ma idan kina wurin a matsayin ki ta mace ana so ki kashe wutan rikicin ne watau ki kasance mai sasantawa. Shi ya sa sau da yawa nakan kasance cikin baƙin ciki inga mata suna bangancin siyasa. Wannan ba halin mace ba ne, domin mace an santa ne da kamalanci. Ba a ce kada ta yi siyasa ba, siyasa ai dole ne a yi. Amma babu bangancin siyasa. Idan kuma ana yi to yakamata ta tsagaita. Ta zama mai sasanta wa tsakanin jama’a ba ta zama mai fitina ba. Saboda haka inaso inga mace mai irin waɗannan halaye.

Bari mu taɓo ɓangaren kwalliya. Wane irin kaya ki ka fi sha’awar sakawa? 
Ni kam nafi sha’awan zani ne da sauran tufafi irin namu na Hausawa. Su nafi sha’awan sawa. Kuma a wasu lokuta saboda zafi a inda muka samu kan mu a nan Lafiya, nakan sa zannuwa masu huji kamar raga watau atamfa ko su shaddodi da kuma hijabi don ka fito acikin martabar ka a cikin mutunci.

Madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.