Kashi tamanin na marubuta na sakin rubutunsu ne a kara-zube – Khadija Dahiru

“Da ana duba rubutu kafin fitar da shi, da an rage ɓarnar da ake yaɗawa a littafan Hausa”

“Ban taɓa sayar da littafina ba”

Rubutu a yanar gizo wani abu ne da zamani ya zo da shi, don haka ba shi muhalli da wasu daga cikin marubuta suka yi bai taɓa zama laifi ba, domin idan ba su bi ba, zai kasance an yi tafiyar ba tare da su ba. A wani vangaren kuwa, za mu iya kiran rubutun yanar gizo sauqi ga masu baiwar ta rubutu, kasancewar ya ba wa kowa damar baje fasahar sa, ma’ana mai kuɗin iya buga littafi da ma wanda ba shi da. Duk da cewa akwai matsaloli da ababen da ba a so ba, waɗanda suke raunana lafiyar adabin Hausa, sai dai za mu iya cewa da yawa daga cikinsu na ƙoƙari gayyan wurin ganin sun fitar da abinda duniyar adabi za ta yi alfahari da su, ba tare da tunanin samun kuɗi ko wata ɗaukaka ba. Khadija Dahiru na ɗaya daga cikin marubutan da suke wannan namijin ƙoƙarin, ba kuma don neman kuɗi ba. A tattaunawar Manhaja da ita, mai karatu zai ji yadda ta faro da kuma wasu batutuwa da za a ƙaru da su. Mai karatu idan ka shirya, Aisha Asas ce tare da Khadija Dahiru:

Daga AISHA ASAS

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.
KHADIJA DAHIRU: Sunana Khadija Dahiru, wacce aka fi sani da official khadeey. An haifeni a 2002, na yi ‘primary’ ɗina a garin Daura, a wata makaranta da ake kira da ‘pace_satters’ inda na yi ƙaramar ‘secondary’ ɗita a ggsss Ajiwa, daga nan kuma na dawo garin Daura, inda na kammala babbar ‘secondary’ ɗita. Bayan nan na jona ‘School of Health Technology’ duk a cikin garin Daura, inda na kammala shekarar da ta gaba ta. na yi karatun addina ma daidai gorgodo cikin yardar Allah har na sauke Alƙur’ani.

Wacce shekara kika fara rubutu?
Na fara rubutun littafai a shekarar 2019, 17 ga watan Fabrairu, inda na fara da littafina mai suna ‘Khadijatul Islam’.

Kasancewar rubutu na da ɓangarori da yawa. Ko a wane ɓangare ne kike da muhalli?
(Dariya) Gaskiya ne. Gaskiya alƙalamina yafi raja’a a rubutun soyyaya.

Me ya sa kika zaɓi ɓangaren rubutun soyayya?
Saboda ita ce abinda ta wahalar da ni a duniya. Shi ya sa na zavi ɓangaren. (Dariya)

Kenan marubuta kan yi rubutu ne a ɓangaren da ya shafi rayuwarsu ne, kamar yadda kika zaɓi ɓangaren soyayya don ta shafe ki?
Bance ko wanne marubuci na zaɓar ɓangaren rayuwarsa ba, iya na wa ɓangaren kawai na sani. Wasu kan ɗauki abinda ya shafi rayuwa ne ta yau da kullum.

Wa za a iya kira da suna marubuci?
Marubuci mutun ne wanda yake amfani da salo daban-daban wajen saurin aika saƙo cikin hikima, sannan ya faɗakar, ya nishaɗantar, ya wa’azantar.

A fahimtar ki, me ya banbanta rubutun maza da na mata?
Mafi akasari rubutun mata ba ya wuce akan soyyaya, inda alƙalamin maza kuma ya fi fito wa da salo irin na yaƙi.

Ko za mu iya jin sunayen littafan da kika rubuta?
‘Khadijatul islam’, ‘Yarima Asad’, ‘Yarima saleem’, ‘Nadiya’ da sauransu. Gaskiya waɗannan dai su ne bakandamiya na.

Shin kina buga littafanki ne ko kuwa kina jerin masu amfani da zamani wato yanar gizo?
Gaskiya har yanzu ban fara buga littafina ba. Amman nan gaba insha Allah.

Wane lokaci kika fi sha’awar yin rubutu?
Da daddare ko tunda safe.

Wasu marubuta da ke buga littafi na ɗora alhakin mutuwar kasuwarsu kan ku masu rubutu a yanar gizo. Shin me za ki ce kan haka?
Bakomai ya kawo hakan ba illa canzawar zamani. Za ki ga shekarun baya da suka wuce ana bada ‘renting’ na littafan Hausa a shaguna da kuma gidaje, inda za ki ga mace sai ta fita da kanta, ta amso, kuma sannan ta koma ta mayar. Amman yanzu zuwan yanar gizo duk ya sauƙaƙa wannan abin. Mace na gida a kwance zata karanta littafi ko kuma ta kai shago a tura mata na sauraro, kinga wannan ba ƙaramar cigaba ba ne. Yanzu mutun ko bai iya karatu ba zai saurara kuma ya gane inda aka dosa, saɓanin littafan da ake buga wa na karantawa kaɗai.

A wurin ki, rubutu sana’a ce?
Gaskiya a wajena rubutun littafin ‘novel’ bai zama sana’a a gareni ba, saboda ban taɓa sayar da littafina ba. Na kasan sake shi ne kowa ya karanta a kyauta.

Waɗanne irin ƙalubale ne marubuta ‘online’ suke fuskanta?
Wasu daga cikin marubuta na fuskantar rashin goyan baya daga wajen makaranta. Ko wacce marubuciya idan ta rubuta littafi a yanar gizo, to fa abu biyo ne tafi buƙata, littafinta ya ɗaukaka, sannan kuma ana mata ‘comment’ da sharhi, wasu za su zauna su rubuta littafinsu, amman sai kiga ba a masu ‘comment’ wannan shi ne babban ƙalubalen marubutan yanar gizo.

Bangon littafin ‘Na Ga Rayuwa’

Za mu so mu ji irin nasarorin da kika samu a harkar rubutu.
Gaskiya ba abinda zance da rubutun ‘Nobel’ sai san-barka, saboda na samu nasarori da dama. Sanadiyyar rubutu ne nasan mutane da dama wanda daidai da rana ɗaya ban taɓa tunanin haɗuwa ko wata mu’amalla da su ba. Yanzu haka na janye rubutun ‘Nobel’ a gefe, yanzu ina rubuta ‘script’ na finafinan Hausa.

Idan marubuci zai fitar da littafi, an so ya nemi masana a ɓangaren su duba masa, sannan kuma a tsaftace rubutun kafin a buga shi. Shin ko akwai wannan tsarin ga marubuta a yanar gizo?
Maganar gaskiya cikin kashi 100, kashi tamanin suna sakin littafansu a kara-zube ne, ba tare da an duba masu ba, domin da ana dubawa, da an rage ɓarnar da ake yaɗawa a cikin littafan Hausa na wannan zamanin.

Ko akwai wani abu da ba za ki iya mantawa da shi ba a harkar rubutu?
Akwai abubuwa da dama da ban mantawa da su a harkar rubutu, ba kamar irin addu’a da fatan alkhairi da makaranta ke min.

Ko akwai wani ƙalubale da kika fuskanta a matsayin marubuciya?
Tabbas duk inda aka samu nasara to tabbas akwai ƙalubale, ba wani ƙalubale ba ne irin yadda wasu daga cikin ‘yan’uwa marubuta suka fara nuna hassada gare ni, wani abu kaɗan yake jira ka yi na kuskure ya fara yaɗa ka.

Muna godiya.
Ni ma ina godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *