Shugaban ƙasar Afirka ta Tsakiya ya bai wa runkunin jinya da Sin ta tura wa ƙasar lambar yabo

Daga CMG HAUSA

Jiya Laraba, shugaban ƙasar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra, ya baiwa tawaga ta 18 ta runkunin jiyya da Sin ta tura ƙasar lambar yabo a fadarsa, inda likitoci 9 suka samu lambar yabo ta jami’an soja, masu aikin fassara da dafa abinci, suka samu lambar yabo ta barada.

A yayin bikin, Faustin-Archange Touadéra ya nuna cewa, ya karrama runkunin da wannan lambar ne, don jinjinawa taimakon da suka bayar da ayyuka masu inganci da suka gudanar, da kuma bayyana matuƙar godiyar jama’arsa ga runkunin. Ya ce, a cikin shekara daya da ta gabata, tawagar ta bai wa iyalan jama’ar wurin makoma da farin ciki bisa ayyukan da suka yi, da inganta hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka da zurfafa daɗaɗɗen zumuncin dake tsakanin jama’ar ƙasashen biyu.

Shugaban tawagar Chen yong ya ce, ya zuwa ƙarshen watan Mayu, tawagar ta yi jiyyar mutane 20874, da yin tiyata 383.

Fassarawar Amina Xu