
Majalisar wakilan Amurka ta amince da ƙudirin da zai dakatar da dukkan wani tallafi da Amurka take bai wa Nijeriya har sai ƙasar ta ɗauki matakan daƙile matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar.
A baya ƙudurin ya bai wa Amurka damar riƙe kashi 50 ne na tallafin, amma a yanzu majalisar ta ƙara shi zuwa kashi 100.
Ɗan majalisa Gregory Stuebe mai wakiltar gunduma ta 17 a majalisar wakilan Amurka daga jihar Florida ne ya gabatar da batun a zauren majalisar ranar Laraba.
Ɗan majalisar wanda ya wallafa bidiyon yadda aka tattauna kan ƙudurin a shafinsa na X, ya ce: “An amince da gyaran da na gabatar kan ƙudurin da ke neman Amurka ta daina bai wa Najeriya tallafi har sai gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan hana yanka Kiristoci.
“Bai kamata a riƙa amfani da kuɗin harajin da Amurkawa ke biya wajen taimaka wa gwamnatin da ta kawar da idon ta ba, yayin da ake sacewa da azabtarwa da kuma kashe Kiristoci ba.
Tun farko majalisar wakilan ƙasar ta buƙaci a riƙe rabin tallafin da aka ware wa Najeriya ne a watan Afrilu, har sai lokacin da sakataren harkokin waje na ƙasar ya ce gwamnatin Najeriya ta ɗauki “ƙwararan matakan daƙile rikicin ƙasar da kuma hukunta masu hannu a ciki”.
