Majalisar Malaman Kano ta sasanta rikicin masallacin Sahaba 

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

A ƙarshe dai Majalisar Malamai ta Jihar kano ta cimma matsaya akan dambarwar masallacin Juma’a na Sahaba dake Kundila a jihar kano.

Bayanin hakan ya fito daga bakin Shugaban Majalisar na ƙasa Sheikh Malam Ibrahim Khalil wanda ya ce bayan zama da dukkanin ɓangarorin masallacin na Sahaba majalisar ta yanke hukuncin na ƙarshe a kan rikicin.

Ya ce mun yanke hukuncin Sheikh Muhammad Bn Othman zai koma masallacinsa na Sahaba, shi kuma Mai Kifi da sauran mutanensa za su cigaba da riƙe na su masallacin na Jami’urrahman

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayyana sakamakon zaman da suka yi ga manema labarai a Kano.

Ya ƙara da cewa Sheikh Muhammad Bn Othman ya amince zai cigaba da jagorantar Sallah a tsohon masallacinsa na Sahaba dake Kundila, yayin da su kuma Mai Kifi za su cigaba da gudanar da harkokin masallacin na Jami’urrahman.

Sannan Malam Ibrahim Khalil ya kuma gode wa dukkanin jami’an tsaro musamman DSS saboda rawar da suka taka wajen tabbatuwar wannan sulhu

By ukarofi