Lookman ya bayyana takaici kan kalaman kocinsa

Spread the love

Ademola Lookman ya ce, ya ji takaicin irin kalaman da kocinsa Gian Piero Gasperini ya yi a kansa, bayan da ya kwatanta ɗan wasan da “wanda ya fi kowa rashin iya buga fenareti” da ya taɓa gani.

Kocin ya yi kalaman ne bayan da Atalanta ta yi rashin nasara a hannun Club Brugge da ci 3-1 ranar Talata a gasar Zakarun Turai, abu kuma da ya sa ƙungiyar ta fice daga gasar da ƙwallo 5-1 gida da waje.

“Abin ɓacin rai ne in yi martani a irin wannan rana, saboda abin da muka cimma a matsayin ƙungiya,” kamar yadda Lookman ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.

Ya ce, ya ji takaicin ware shi kaɗai da kocin ya yi, duk da irin hazaƙa da kuma ƙoƙarin da yake yi wajen ganin ƙungiyar ta yi nasara.

By ukarofi