Tare da BASHIR MUDI YAKASAI
Ga masu Shugabanni masu hangen nesa a kasarsu, kamar yadda Kamus na Hausa ya yi tarihin kalmar Turanci ‘Focus’ da ya ‘mai da hankali kan” wani abu, da sai mu ce sambarka da fadi-tashin da Majalasar Dinkin Duniya ta kwashe sama da shekaru 30 kan ‘sauyin yanayi’, wanda ya jefa wasu daga cikin kasashen duniya ka kanakayi bisa gonaki, a wasu guraren kuma a ka sami kamfar ruwa, wanda ya kawo qarancin abinci ga bil adama da dabbobi da tsintsaye.
Sauyin yanayi shi yake haifar da kadawar iska daga teku zuwa doran kasa, inda ta ke barna ta duniya miliyon daloli da halaka rayuka masu tarin yawa, haka kuma wutar daji duk da taran dangi na ma’aikatan kasha gobara, amma wutar nan saita gagari kundila. Mai yawa daga girgizar kasar da aman wuta daga duwatsu (earthquake and volcano) suna faruwa ne dangane da sauyin yanayi. Wadan nan zantuka daga masana musamman masanan labarin kasa (geographers) da masu ilimin sanin ma’adinai (geologist) da kuma masu ilimin sararin samaniya (Climatolist).
Babu mai ja da ilimi, amma ina masu ilimin suke da suna kallo wasu ‘yan kalilan suna wasa da hankulan jama’a a sunan Damokaradiya ana yada akudar ‘yanci tara abin duniya, mai mulkin jama’a ya kasance sai mai kudi, mai sarautar gargajiya sai mai kudi, malamin addini sai kudi, sarkin noma sai mai kudi shugabannin tsaro (‘yan butuniya), masu tsaron rayuka da dukiyar al’umma a gari suma yanzu sun kasance sai masu kudi. Hatta dan kasuwa ya tashi daga me saye da sayarwa ya koma mai tara kudi a garin su ko a kasar sa koma a nahiyar da ya fito har ma ya rika alfahari ya fi kowa kudi a duniya. Babu sauran jinkai a tsakanin al’umma.
Saboda mulkin dimukradiya babu wata kasa a duniya da ke cikin kwanciyar hankali. Misali; a kasar sai wani ko wata tako ya kashe wani ko sun kashe kansu babu gaira babu dalili illa dalilin kudi. A Amurka mutunci ya koma kudi, mutum mai ‘hankali’ zai siyar da mutuncinsa, saboda kudi. Duk mai bibiyar kafofin sada zumunta za ka cika da rudani (confuse), saboda halin da ko dabbobi na gida ko na daji ba sa aikatawa, amma dan sdam ya na aikatawa da sunan ’yanci, sai ka firgita, ka na tambayar kanka Ina duniya ta dosa!
Mun yi wannan doguwar shimfuda, domin mu kalli Nijeriya da Sauran kasashen Afirka, Saboda wannan mulki na Damokaradiya mai cike da rudani da sunan ‘yanci (freedom), wato raba duniya da gaskiya da amana da jinqai da godiya da juriya da yakana da kunya da ruko da addini, yan zu ba daya. Kowa da kowa daga shi sai matarsa da ‘ya’yansa, idan ma da su. Saboda ta kai ta kawo da ko ‘ya’ya sun zama shara, bola, juji domi kuwa a titi ake samar da su da zarar an haifesu sai a kais u kwandon shara, uku daga ciki goma anan rai yak e halin sa, su kuma bakwai (7) su qara a bola ko juji, masu tsahon rai su biyu ko daya karewa a gidan renon jarirai.
Ta kai intaha, Saboda wannan tsari na cikin wannan mulki na Damokaradiya, mai kururuwar ibilis da sunan wannan ‘yanci Daga Cikin ‘ya’ya ko kuma muce mutane goma (10) bakwai (7) daga cikin su ba su sani iyayen sun a hakika ba, wato mahaifan (Baba da Inna) ba, sai dai mariki. Binci key a tabbatar da cewa, ko Babar su, shi doka ta Amurka ke kira ‘Single Family’
Kuma abin takaici kasha tamanin da biyar (85%) wadan nan ‘Single family’ din dukkan su bagaggu ne (Alcaholist). Idan har Nijeriya da take fitar da makamashin danyan ma fetur sama da ganga miliyan guda a kullum, kuma a sayar da wannan man fetur ba a maganar gas da duk sauran dangogin sa a sama da Dalar Amurka saba’in (70) a kullum amma ‘yan Nijeriya da kasha Arba’in da biyar (45%) suke kwana da yunwa, saboda da kyar suke samun Dala daya duk da cewa yana da iyali sama da goma (10). Tambayar a nan itace, yaya dan kasa zai rayu babu wannan hajja a kasuwa
Shugabannin Nijeriya tun daga 1960 zuwa yau ba sa mayar da hankalin su ga ‘yan kasa sai a kan su, su da iyalin su, su yi gidaje da motoci da jiragen sama da ruwa domin ke ce raini. Burun su a ce ‘ya’yan sun yi karatu a birnin Landon da sauran biranan duniya a USA da Canada da UAE da kuma China. Rashin ‘Focus’, wato hangen nesa na shugabanni shi ya sa ake barin mu a baya. Idan har da hangyen nesa a kasannan da baza mu bar noma da nkiwo a kasarnan ba har ta kai miliyoyin mutane suna kwana babu abinci.
Tun da kora ta kai bango, matsalar da take faruwa a kasa irin ta mu shine yaki tsakanin me shi da marar shi yaki tsakanin gwamnatoci da ‘yan tawaye da za su zo da akidu marasa kan gado, misali ‘yan Boko Haram, masu garkuwa da jama’a sai ambiya kudade kafin a sako su, ko ‘yan fashin daji kamar muke jin su a zamfara da kebbi da sokokto da katsina da kudancin kaduna da zaria da wasu Bangarori na jihar Niger, Nassarawa da kuma Taraba.
Wajibi ne ga wannan gwamnatin ta APC ta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu su sake tunani su kirawo sauran jam’iyu na hamaiya cewa, ga fa gobara ta kunno ka daga kogi yaya za a kasha ta tun kafin ta iso ga tudu. A fara daukar mataki na gaggawa. Shirin ya fuce na zantuka, Shirin ne na aiki gadan-gadan dare da rana. Hankali gaba daya ya koma ga ma’adinai, noma da kiwo, kimiya da fasaha da kuma sauyin fasalin al’ada ga zuwa tattalin arziki.
Idan Nijeriya za ta mayar da hankalinta ga ma’adinai zata ci riba Tama, da Azurfa, da Bakin Qarfe, da Gorar Ruwa, da Zinare da Yashi da Tabo (laka /yunbu) da barbarkiya da jan Gargari da sauran duwatsu na alfarma Har da ma’adanai Yurenium. Jihohin nan 36 har da birnin taraiya Abuja suna da ma’adinai nan 36 har kuma masana daga ciki gida da kuma na waje sun tabbatar da cewa, idan Nijeriya zata mayar da hankalinta kan ma’adinai nan da shekara ta 2050 sai Nijeriya ta zama Aljanar Duniya, Kamar yadda muke ji a qasashen UAE a yanzu har ma ana cewa fiye.
Babu wata qasa a Afirka da take da yancin da a iya noma duk wata kwaya da dan Adam ya ke a doran duniya misali’ Alkama, Shinkafa, Masara Dawa Gero, Maiwa ga kuma rogo, Doya, Dankali, Dankalin Turawa (kwambitar), wadan kadai sun isa mu ciyar da kammu mu kuma ciyar da sauran Nahiyar Afirka. Idan dai har Yukiren da tsibirin Indonisiya da Malesiya da. KumaTaiwan za su bawa duniya Alkama da Shinkafa da kjma Sha’ar
Duk da rashin mayar da hankali ga al’amuran kasa ga Shugabanni za mu iya yabawa Shugan Kasa Asiwaju Bola Ahmef Tinubu da ya zo da ma’aikatar Fasahar Al’adun Gargajiya da kirkira zuwa sauya su zuwa ga, Al’umma, wato (FMACCE), wannan ma’aikata idan ta dage ta aiwatar da tsare-tsare da aka tanadar mata a masana’ antun fasaha na gargajiya kamar kira, jima, saka, Rini, Dukanci, Sassaqa. Bayaga haka ga wasanni da za a kyautata su za su kawo kudi mai tarin yawa ga ‘yan kasa.
Wannan su ne Dambe, kokawa, shadi langa, turna, Allanbaku- Allankarbe, Shanci. kade-kade da Bushe- Bushe da kuma Raye-Raye ko kasar Habasha ta kyale mu, wacce zata kara da mu ai sai kasar sin, wato china. Muna da abubuwan da za mu nunawa duniya su bamu kudade masu ciwo. Nolywood da Kannywood suna samawar ‘yan Nijeriya aikin yi daban-daban sama da sittin tun daga masu rubuta labari da masu shiryawa da masu bayar da kudade domin a yi finafinai da kuma Shirye-shirye na rediyo da talbijin da kafofin sadarwa na zamani. Yan zu a Nijeriya samari da ‘yan mata sama da rabin miliyan (500, 000) Suke cin abinci da wannan sana’a a kullum.
Da Nijeriya zata mayar da hankalin ta fannin ilimin kimiya da fasaha cikin manya-manyan yaran kasa, wato harshen uwa (Hausa, yoruba da Igbo) na tabbatar muku Nijeriya za ta karbi gaba a fannin kere-kere kamar yadda muke gani a sha’anin kiwon lafiya a masar da cuba da kuma Habasha (Ethopia). Sun sami wannan garbasa ne saboda amfani da harshen uwa, ta haka ne Jamus, Faransa Rasha, Iran kai da duk wata qasa da ta gawurta ta samu kantaa fagyen ilimi ta na yinsa da harshen uwa.
Babu inda za mu idan muna neman ilimi da harshen wasu wannan shine mulkin mallaka domin ba mu da sirri, wanda ake cewa, ” Shuka a idan makwarwa”.
Shawara ta karshe ita ce ‘yan Siyasa gabadayansu sun yarda cewa wannan kasa da al’ummarta sune a gaban su. Yan kasa su zasu tsara abin da suke so a qasarsu duk dan siyasar ko jam’iyar Siyasa ta sauka daga wannan tsarin ‘yan kasa sai su saukata daga kan kujera ta. Wato dai a dora wannan kasa bisa tafarkin kishin kasa- Nationalism da kuma kishin jama’a ‘Patriolism’.
Kishin kasar da kishin al’umma da muke magana akai shine gina al’umma da tsarin mulkin Nijeriya yake magana akan sa da ya kira ‘Human development’. Wato dan Adam ya fi karfin abinci da abin sha da mahalli da sutura da ilimi ‘ya’yan sa da lafiyarsa da ta su. Kama an cika shi Tawalu’u (Humble) wato dai yana cike da tausayin dan Adam – Humanitarian person.
