Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Masu Kamfanonin Wallafa Jaridu ta Nijeriya, wato ‘The Newspaper Proprietors’ ta bayyana kara kudin jaridu a sabuwar shekara.
Association of Nigeria (NPAN)’ ta bayyana cewa daga ranar 2 ga watan Janairun 2024 sabon farashin jaridu zai fara aiki a duk fadin aasar nan.
Babban Sakatare na Kungiyar ta NPAN, Feyi Smith ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a Abuja cikiin makon da ya gabata.
Mr Feyi ya ce, “Kungiyar mu da dauki wannan tsattsauran mataki ne bisa nazarin da ta yi na matsin tattalin arzikin da mambobin mu ke ciki, musamman na kayan buga jaridun.”
Ya kara da cewa, tashin gwauron zabin da kayan aiki ke yi, sannan ga faduwar da darajar Naira ke yi, wanda ya sanya yanzu sam ba sa samun wata riba a harkokin nasu, musamman a wadannan shekarun.
Sai dai duk da tashi da hauhawar da kaya ke yi a shekarun nan, Mr Feyi ya bayyana cewa yau shekaru hudu ke nan ba su yi karin farashin jarida ba, duk da kuwa kudin kayan aiki sun nunka nunkin-banunkin.
Daga nan shugaban mawallafa jaridun ya yi fatan cewa masu karatun jaridu za su fahimce su a wannan sabon farashin da za su sanya, su sani dole ce ta sa su yin wannan kari.
Ya ce, “Muna fata masu karatun jaridu za su fahimci dalilan mu na yin wannan kari, musamman ganin cewa muna kokari wajen zamanantar da yanayin wallafa jaridun, don samun jaridu da rubutu masu inganci.”
