Emefiele, daga kukan targaɗe an koma karaya

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HAKAYA

Hakika duk mai bin bayanan da su ka biyo bayan cika ka’idar da ta sa tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Godwin Emefiele ya samu ficewa daga gidan yarin Kuje zai iya fahimtar tafiyar sa gida tamkar hutun jaki ne da kaya a ka. Akasarin wadanda su ka samu beli na samun sararawa don in ma akwai dace shikenan sun huta da zaman gidan yari. A wasu shari’un ma za ka taras wani har rai ya yi halin sa ba a gama sauraron karar da a ka shigar da shi ba.

 In ka debe irin Emefiele da ya yi gwamnan babban banki, kalilan ne daga jami’an gwamnati za a labta mu su ka’idar beli ta Naira miliyan dari 300 da kuma mutum biyu masu tsayawa su din ma ke mallakar kadarar da ta kai wadannan makudan kudin.Alamu sun nuna indai don irin aikin da kudi za su iya yi ne a samu sauki to ba matsalar Emefiele ba ce. Manyan lauyoyi ma sun tsayawa Emefiele don ya fito ya tafi gida.

 In mun tuna cajin farko ma kamar ya saba da abun da mutane ke sa rai inda a ka tuhumi Emefiele da mallakar bindiga ba lasisi. Daga bisani an kawo wani caji da ya shafi wasu kudi amma nan ma mutane ba su ji abun da su ke tsammani na miliyoyin dala ko biliyoyin Naira ba. A yanzu ta baiyana bincike ne da wa imma ba a gama ba ko an yi tuhumar farko ba tare da samun shaidun da za a gurfanar da Emefiele a gaban kotu ba. Ga shi dai an tabbatar akwai ayoyin tambaya kan Emefiele amma ba a tono bayanai da za su iya gamsar da alqali ya yi ma sa hukuncin mai babban laifi ba.

Fitar Emefiele ke da wuya sai ga bayanai cikin rahoton kwarerren mai binciken ayyukan babban banki karkashin Emefiele da shugaba Tinubu ya nada Jim Obazee da ke nuna zargin da a ke sa ran ji na wawure dukiyar Nijeriya da Emefiele ya yi ya jibge a ketare. Kazalika bayanai ma somin tabi ne daga rahoton da mai binciken ya gabatarwa shugaba Tinubu.

Tsohon gwamnan babban bankin Njeriya CBN Godwin Emefiele ya samu kan sa har ma ya yi barazanar daukar matakin shari’a kan mai bincike na musamman Jim Obazee.

In za a tuna mai binciken wanda shugaba Tinubu ya nada don duba aiyukan Emefiele, ya fito da rahoton zargin Emefiele da mummunar badakala ta tarihi da ta hada da tura biliyoyin Naira na Nijeriya ketare.

Obazee ya nemi a dauki mataki kan Emefiele don ya na da hannu wajen bude ma’ajiyun kudi 593 a manyan kasashe turai da zuba kudin jama’ar Nijeriya a ciki.

Emefiele ya ce mai rahoton ya bata ma sa suna kuma duk zargin da a ka yi ma sa ba gaskiya ba ne, don haka ya na tunanin daukar matakan shari’a don wanke kan sa.

Babban mai binciken Mr.Jim Obazee ya baiyana cewa an gano tsohon gwamnan babban banki Godwin Emefiele da wasu jami’an bankin sun wawure makudan kudin Nijeriya su ka jibge su a bankunan ketare.

Bayanin ya gano ma’ajiyun banki 593 da Emefiele ya bude ta barauniyar hanya ya jibge kudin a Amurka, Burtaniya da kuma kasar Sin.

Hakanan an samu fitar da dala miliyan 6.23 kimanin Naira biliyan 2.9 da Emefiele ya zare su ta hanyar almundahana.

Mr. Obazee ya ba da shawarar a gurfanar da Emefiele da mataimakan sa da su ka taimaka wajen sace kudin banki a kotu.

Mr.Obazee ya gabatar da rahoton sa ga shugaba Tinubu da bayanai filla-filla na ma’ajiyun kudin Emefiele ta hanyar badakala a ketare da ya ke bukatar a garzaya kotu don cajin tsohon gwamnan da zai iya kai wa ga hukunta shi. Don haka ya nuna Emefiele bai gama yarfe gumi ba bayan fita daga gidan yari sai ga sabuwar babbar tuhuma a kan sa da za ta iya maida hannun agogo baya. Ni dai ban yi mamakin barazanar Emefiele ta garzayawa kotu don neman hakkin abun da ya zayyana da neman bata ma sa suna.

Dalili na kuwa na tuna tun ya na kan kujera ya dau mataki kan wani babban mai binciken kudi Dr. George Uboh wanda ya zargi Emefiele da wawure biliyoyin Naira. Matakan Emefiele kan Uboh ya sa a ka ajiye Uboh na dogon lokaci a gidan yari inda da kyar ya samu kan sa bayan jajircewa a kotu.Uboh na daga masu binciken da ke da ra’ayin matukar Nijeriya za ta tsaya wajen gano kudin ta da ke boye, to ba ta bukatar nemo ba shi don samun kudin da za a yi amfani da su a kasafin kudi.

Sabuwar magana da ka iya hana Emefiele runtsawa ita ce yadda Jim Obazee ya bankado yiwuwar tsohon gwamnan babban banki CBN Godwin Emefiele ne ya kafa bankin Titan Trust da ya sayi hannun jarin bankin UNION da kudin haram.

Obazee a rahoton da ya gabatarwa shugaba Tinubu ya ba da shawarar gwamnati ta karbe bankunan biyu don da kudin baitul mali a ka mallake su. Ta kan yiwu wani sashe ne na binciken ne ma ya baiyana ga jama’a ta kafafen jaridu.

Lauyan tsarin mulki Barista Mainasara Kogo Umar ke bayanan hurumin shugaban kasa na kafa kwamitin binciken “Sashe na 21 na tsarin mulkin Nijeriya ya ba da hurumin kafa kwamitin da kare ayyukan Jim Obazee. Ya na da kyau Obazee ya tsaya kan aikin na. A gaggauta a gano duk masu hannu a badakalar nan da hukunta su kuma in ta kama a gaiyato tsohon shugaban kasa ma.”

Martanin da shugaban bankin TTB Tunde Lemo ya yi ta hanyar jaridu cewa sam batun ba gaskiya ba ne, ya sa ofishin mai binciken gayyatar sa da mutum biyu masu hannayen jari don sauraron bayanan su a gaban masu bincike da za su zauna a ofishin bayanan sirri na ’yan sanda da ke daura da helkwatar rundunar ’yan sanda a Abuja.

A baya ma kwamitin ya gayyaci masu hannun jarin inda amsa tazo daga TTB cewa akwai uzurin rashin lafiya ko bas a kasar amma da zarar sun dawo za su amsa gayyata.

Mr. Obazee ya ce duk bayanan da bankin TITAN ya gabatar akwai matsala a ciki don an je har Dubai a ka gano kamfanin da ya ba da kudin sayan hannun jarin ba shi da ofishin da ya ce daga nan ya ke aiki.

Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’aziz Abdul’aziz ya ce ba a karvi rahoton a hukumance ba sai an kammala tattara dukkan bayanai. Abdul’aziz ya ba da tabbacin cewa da zarar an mika cikekken rahoton ga shugaba Tinubu za a dau mataki a kai ta hanyar kwato kudin jama’a da wasu tsiraru su ka wawure.

A takaice dai an gano wani babban mai ba da lamuni ba ranar biya a boye a lamarin bankin na TITAN inda kuma Obazee ke ganin Godwin Emefiele ne.

Barista Mainasara Kogo Umar da ke bin binciken, ya ce ya zama wajibi a dau matakai don ceto dukiyar kasa.

Ofishin mai binciken ya yi gargadin cewa matukar mutanen da a ka gayyata ba su zo ba hakan ya nuna sun sarayar da jarin su ko dukiyar da su ka ikirarin ta su ce su ka zuba a bankin ga gwamnati.

Rahoton Obazee ya nuna mutum biyu Rahul Savara da Cornelious Vink ne ‘yan barandan da Emefiele ya yi amfani da su wajen mallakar bankuna 3 da su ka hada da Titan, Union da Keystone. Duk bankunan uku Obazee ya ba da shawarar gwamnati ta karbe su.

Rade-radin bayan fage na nuna ko an samu Emefiele da laifi to za a iya yin mutuwar kasko ne don yadda hannun wasu da shi kan sa Obazee ya baiyana na cikin badakalar. Mutanen nan ka iya fin na cikin banki kadai har ma za a iya samun na wajen banki kamar yadda Barista Mainasara ke son gayyato jami’an tsohuwar gwamnatin Buhari da su ka hada da tsoffin ministoci matukar an ga hannun sa a wannan zargi na mummunar almundahana.

Mainasara bai bar jami’an sashen zartarwa ba ya ce har ma da wasu ’yan majalisar dokoki ka iya zama da hannu a wannan binciken da a ke gudanarwa. Gaskiya biri ya yi kama da mutum don gabanin a dakatar da Emefiele daga kujera sojoji ne ke kula da tsaron sa musamman bayan labarin da a ka musanta cewa jami’an rundunar farin kaya sun yi yunkurin cafke shi. Akwai mamaki a ce jami’i mai gaskiya a tsakiyar Abuja ya bukaci sojoji ko a tura sojoji su kare lafiyar sa.

Kammalawa;

Shawara kawai a yi fatar Jim Obazee zai tabbatar da gaskiya bisa nauyin da a ka dora ma sa don ta wata ruwayar an ji wadanda a ke tuhuma na son a sulhunta a siyasance. Akalla dai ya dace gwamnatin Tinubu ta shafawa fuskar ta toka ta yi dirar mikiya kan duk wanda ya yi babakere da dukiyar kasa. Daukar irin matakin ba sani ba sabo ne zai zama darasi ga wasu da ke jiran samun mukaman gwamnati don wawure kudin jama’a da zummar yin bushasha a kasashen ketare

By Editor