Makarantar Al-Azhar na ƙarfafa ɗalibanta zama masu ƙwazo da ikhlasi, inji Daraktocinta

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Makarantar Al-Azaha a jihar Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai da raba kyautuka ga waɗanda suka yi ƙwazo a yayin taron a harabar makarantar ranar Asabar da ya samu halartar ɗinbin iyaye da sauran manyan baƙi.

A bayanan su game da taron, Daraktocin makarantar Farfesa Binta Tijjani Jibrin da Farfesa A’ishatu Abdu Isma’il da suka kafa makarantar sun bayyana irin ɗinbin gudunmuwa da makarantar ke bayarwa ga bunƙasa cigaban ilimi.

Farfesa A’ishatu Abdu Isma’il  ɗaya daga  daraktocin ta bayyana cewa taron ana shirya shi ne kowace ƙarshen shekara na zangon karatu, saboda a ƙarfafa gwiwar sauran yara domin su a makarantar Al-Azhar abinda suka fi ƙarfafawa shine koyar da yara su zama masu amana da Iklasi shine ya sa suke  koyawa yara karatu da tarbiyya sosai na addinin musulunci.

Ta ƙara da cewa suna ƙoƙarin cusa tarbiyya ga ɗalibai   ta hanyar dora  akan tsayawa akan gaskiya  shi yasa ma ba su yarda da satar amsar jarabawa ba a makarantar duk abinda ake  gani na kwazon ɗaliban su, haka  yake  haka aka koya musu, kuma ana samun nasara,tun daga   kafa makarantar  suna bibiyar ɗaliban su da kyau  waɗanda suka je jami’o’i da manyan makarantu bayan sun gama sukan samu  ɗalibai  na zama kan gaba a  masu kwazo a ajin su 

Farfesa A’ishatu Abdu Isma’il  ta ce ana samun   ɗaliban da suka fito daga makarantar  sun gama jami’a  ko manyan  makaranta  da sakamako mai kyau  yawancin su  wasu sun zama likitoci ,lauyoyi injiniyoyi da manyan ma’aikata a wurare da yawa kuma ana samun su da kwazo da tarbiyya da rikon Amana a duk inda suka sami kansu.

Ita ma a nata bayanin  Farfesa  Binta Tijjani  Jibrin  ta ce  in ana maganar tarbiyya, mutunci da riƙon amana ana samun sune ta tushen  koyarwar addinin musulunci  a matsayin su na musulmi  domin shine ginshiƙi don haka ganin ilimi na zamani abu ne  mai  muhimmanci  shi yasa  suke gyara inda suka ga wani abu da bai dace da tarbiyya  ba  a ciki sai su cire duk wani abu da zai ɓata tarbiyya sannan su kawo abinda ya dace su koyawa  ɗalibansu wannan ta sa  suke haɗa ilimin addini dana zamani a makarantar.

Ta ce tunda aka kafa makarantar  shekara  ta 2000 sun ɗauki  ilmi da  bayar da tarbiyya a matsayin  haƙƙi ne na iyayen yara da malamai da makaranta don haka ake haɗa hannu don tabbatar  da.tarbiyya   suna da hanyoyi da yawa da suke shigo da iyaye a cikin  harkokin makarantar domin  su taya su wannan aiki,  suna kuma samun goyon bayan iyayen yara   kashi 90 bisa  100.

Farfesa Binta Tijjani Jibrin ta ce suna da tsare- tsare na tallafawa ya’yan malamai dana ma’aikatan makarantar  da ya’yan al’ummar  da suke maƙotaka da  makarantar  suna kuma  da  tsarin tallafawa  wasu makarantun  Gwamnati da suke kusa dasu ta hanyar horar da malamansu da tallafi ga makarantun suna  baiwa yara masu kwazo da iyayensu basu da hali  tallafin kudin makaranta “scholarship” 

Farfesa Binta Tijjani Jibrin ta yaba matuƙa da irin goyon baya da gudunmawa  da iyaye da malaman makarantar suke bayar wajen kulawa da ɗaliban da hakan na taimakawa wajen  fice samar  da makarantar ta ke wajen bada ingantaccen ilimi ga ɗalibai 

Shi ma shugaban kwamitin iyaye  da malamai na makarantar Al-Azhar.Alhaji Ibrahim ɗanyaro, shugaban Dattawan Kasuwannin Sabon Gari da Singa yace suna farin ciki da taron yaye ɗaliban domin rana ce da makarantar ke nuna ta kai matsayinda yakamata a wajen bayar da  tarbiyya  da bada ilimi.

Ya ce Makarantar  da farko ta yi suna ne wajen bada ilimin zamani amma yanzu tana ƙoƙarin  haɗawa da ilimin addinin Musulunci wanda dama shine abinda ya kamata a samu ‘ya’yan Musulmi a kai su zama ‘yan boko kuma masana akan addini ta wannan za a ci riba biyu an haɗa ilimi biyu da zai amfanar da al’umma.

By ukarofi