Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rashin jituwa tsakanin al’umma mazauna Jajin jihar Kaduna da jami’an rundunar soji da ke yankin ta ƙara ƙamari biyo bayan rushe wa mutanen gidajensu da sojojin suka yi.
Mazauna wurin sun ce sojoji a ranar Juma’ar da ta gabata, sun dirar wa al’ummar ƙaramar hukumar Igabi tare da mai da gidajensu ƙasa duk da umarnin kotu da ya dakatar da rundunar daga rushe musu gidaje. Wannan lamari dai ya bar da yawansu babu gida cikin damuwa.
Sai dai rundunar sojin ta musanta zargin da ake yi mata.
Mazauna dama a yankin da suka haɗa da: Ungwan Yohanna, Ungwan Aboki, Sabon Ungwan Loya, Ungwan Railway, and Ungwan Alhassan, sun daɗe suna ja-in-ja tsakanin su da rundunar tun shekarar 2020.
Wannan ja-in-jar ta samo asali ne bayan da sojoji suka saka zagaye katangar barikin sojin. Mazauna yankin sun nuna rashin amincewarsu saboda an kutsa cikin gonakinsu da suka gada tun iyaye da kakanni. Sun zargi rundunar da ƙwace musu fili ba tare da bin mataki na shari’a ba.
Mai shari’a Hannatu Balogun ta babbar kotun jiha ce ta sha ba da umarnin ƙauracewa gini a kan filin tare da ba wa sojoji umarnin barin mazauna wurin su yi amfani da filayensu.
Sai dai lauyan waɗanda ke tsaya wa al’ummar Kimi Appah, ta shaida wa wakilinmu cewa rundunar sojin Nijeriya ta yi watsi da wannan umarni na kotu tare da rushe musu gidajensu da kama wasu daga cikinsu.
Mista Appah ya ce waɗanda yake wakilta da dama ne suka shaida masa cewa an rushe musu gidajensu ba tare da na ba su notis ba ko diyya. Haka kuma an kama wasu daga cikinsu wanda ya bayyana hakan da ƙoƙarin razanarwa da kama-wuri zauna da sojojin ke ƙoƙarin yi.
Appah ya yi kira ga gwamnatin tarayya da manyan hafsoshin tsaro da su sa baki yana mai ba wa sojojin shawarar su mutunta umarnin kotu da gujewa ɗaukar kowanne irin mataki a kan al’ummar.
Sai dai rundunar soji ta musanta rushe gidajen da ake magana wanda ta ce batunsu na gaban kotu.
Mai magana da yawun barikin sojin, Olusegun Abidoye, wanda kaftin ne, a ranar Asabar, ya ce, rundunar sojin ta rushe wurin masu sayar da ƙwayoyi ne da ke ayyukansu a yankin wannan barakin sojin.
Ya ce sun miƙa waɗanda ake zargi hannun hukumomin NDLEA domin ɗaukar matakin da ya kamata kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya rawaito.
Mista Abidoye ya ce rundunar ta damu ne kan bunƙasar laifuka musamman na sayar safarar ƙwaya a wurin da suka rushe.
“Wannan ya haɗa da hanyoyin layin dogo da Unguwan Loya, Unguwan Aboki, Unguwan Alhaji and Unguwan Alasan.
“Waɗannan mutane a yayin da sukan yi wa wa rundunar wasu ayyuka, sukan kuma zama barazaz ga tsaro.”
“Mafi yawan suna zaune a cikin mutanen a yayin da suka zama barazana ga su al’ummar da rundunar sojin, in ji Mista Abidoye.
Ya kuma ce bayanan sirri da suka samu ya nuna akwai sansanin manyan dilolin ƙwaya da ke zaune a wurin.
A cewarsa wannan na ba da gudunmowa wajen ƙaruwar yaran sojoji da waɗanda ke zaune a barikin sojin da ke shan miyagun ƙawayoyi.
Ya ce rundunar ta gudanar da bincike da sa ido inda ta tabbatar da ana safarar miyagun ƙwayoyi musamman a yakin filin jirgin da Unguwan Loya.
“Manyan dilolin ƙwaya 15 ne suke gudanar da ayyukansu na safar ada sayarwa da rarraba ta a ciki da wajen barikin.”
“Wasu daga cikin ƙwayoyin da ake safararsu sun haɗa da: hodar iblis, skunk, Eɗol, ice, crack cocaine, tiramadol, da sauransu,” inji Mista Abidoye.
Ya ce, sun yi kamen ne domin rage ta’azzarar wannan matsala a yankin.
Game da zargin rushe gidajen fararen hula da wasu kafafen yaɗa labarai suka yi, mista Abidoye ya ce, zargin ba gaskiya ba ne “duk da hotunan sojoji” da aka gani saboda ba su aikata hakan ba.
Mista Abidoye ya ce, su ma mazauna yankin sun saɓa wa umarnin kotu ta hanyar yin sabbin gine-gine da barin wani kamfani ya riƙa haƙar wasu ma’adanai daga filayen.
Abidoye ya ce, sai dai suka shigar da kokensu na neman kotu ta hana mutanen da kamfanin daga haƙar wannan ma’adani zuwa lokacin da za kammala shari’a.
Game da zargin katse musu wutar lantarki ga al’ummar da ke kewayen barikin, mista Abidoye ya ce babu hannun sojoji wajen wannan lamari.
Barikin soji ta Jaji muhimmiyar bariki ce ga rundunar sojin Nijeriya wacce ke ɗauke da makarantar sojoji da kwalejin sojoji da manyan ofisoshi da cibiyar dakarun sojin ƙasa da cibiyar tattauna zaman lafiya ta Martin Luther Agwai da sauransu.
