Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Sakataren ƙungiyar Bunƙasa Harshen Larabci da Al’adunsa ta ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Malam Adamu Yakubu Saleh, ya bayyana cewa makarantar koyar da Larabci da Addinin Musulunci ta maza a Birnin Kudu na fama da matsanancin hali.
Ya ce makarantar na fuskantar ƙarancin azuzuwa, rashin ofishin shugabanci, ɗakin taro da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Ya bayyana hakan ne yayin bikin Ranar Bunƙasa Harshen Larabci ta Duniya da aka gudanar a Birnin Kudu, Jihar Jigawa.
Malam Adamu Yakubu ya ce duk da Birnin Kudu na gaba wajen yawan yara da matasa masu koyon Larabci a Jihar Jigawa, makarantun Larabci musamman na mata na buƙatar gaggawar tallafi daga gwamnati da masu ruwa da tsaki.
A nasa jawabin, Hon. Ado Madu Sale, mai bai wa Gwamnan Jigawa shawara kan ilimin matakin farko, ya nuna takaici kan rashin halartar manyan masu hannu da shuni wannan taro mai muhimmanci, duk da irin kulawar da Gwamna Umar Namadi ke bai wa ilimi.
