Daga RABIU SANUSI a Kano
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano da ya gaggauta janye jami’an tsaro da aka jibge a Fadar Nasarawa, inda tsohon Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ke zaune a halin yanzu.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da Hukumar Tsaron Unguwanni ta Jihar Kano (Neighbourhood Watch Corps), mallakin gwamnatin jihar, da aka gudanar a Kano.
A cewarsa Muhammadu Sanusi II shi ne kadai halastaccen Sarkin Kano, yana mai gargaɗin cewa ƙirƙira ko ci gaba da ɗaukaka wasu cibiyoyin gargajiya masu zaman kansu na iya kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Tsohon gwamnan ya jaddada cewa amfani da jami’an tsaro wajen tilasta wani sarki ba abin karbuwa ba ne yana mai cewa hakan na iya kara ruruta wutar rikici da tayar da hankalin jama’a a Kano.
Ya kuma bayyana cewa daukar matakin ba Aminu Ado Bayero masauki a Fadar Nasarawa ya sabawa al’adu da martabar masarautar Kano, wadda ke da tarihi mai tsawo da daraja a idon al’umma.
Kwankwaso ya yi kira ga dukkan hukumomin tsaro da su yi aiki bisa doka da umarnin gwamnati tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya haddasa tashin hankali ko tayar da tarzoma.
Wannan kira na zuwa ne yayin da rikicin shari’a kan masarautar Kano ke ci gaba lamarin da ke ƙara janyo muhawara da damuwa a tsakanin mazauna jihar da sauran masu ruwa da tsaki.
